Zargin fyade: An dakatar da tantance Babban Alkalin Kotun kolin Amurka
Mista Brett Kabanaugh shi ne mutumin da Shugaba Donald Trump ya mika sunansa ga Kwamitin Harkokin Shari’a na Majilisar Dattawan Amurka domin a tantance shi a matsayin Babban Alkalin Kotun kolin kasar. Amma bayan kwamitin ya gayyace shi tare da yi masa tambayoyi, kwatsam sai ga labarin wata mata mai suna Christine Blassey Ford da […]

Mista Brett Kabanaugh shi ne mutumin da Shugaba Donald Trump ya mika sunansa ga Kwamitin Harkokin Shari’a na Majilisar Dattawan Amurka domin a tantance shi a matsayin Babban Alkalin Kotun kolin kasar.
Amma bayan kwamitin ya gayyace shi tare da yi masa tambayoyi, kwatsam sai ga labarin wata mata mai suna Christine Blassey Ford da take koyarwa a Jami’ar Palo Alto da ke Jihar Kalifoniya, ta yi hira da jaridar Washington Post inda ta shaida wa jaridar cewa mutumin da ake son tantancewa ya taba yin yunkurin yi mata fyade shi da wadansu abokansa lokacin suna makarantar sakandare shekara 36 da suka wuce.
Matar a cikin hirar ta ce Kabanaugh da abokansa sun kai ta cikin daki kuma suka yi kokarin cire kayan da ke jikin ta, amma ba su yi nasarar haka ba.
Ta ce wannan abin ya faru ne a Jihar Maryland a lokacin da suka tafi wurin wani bikin holewa. Sannan ta bayyana cewa a lokacin shi da abokansa da suka yi wannan yunkurin ta dauka ma za ta mutu ne. Ta ce lokacin da ta yi yunkurin kuwwa sai suka sa hannu suka rufe mata baki.
Koda wannan batu ya kai kunnen kwamitin, sai suka dage zaman jefa kuri’a kansa suka ce sai sun bincika tare da gano gaskiyar wannan batu. Yanzu haka dai an dage jefa kuri’ar amincewa da shi sai sun binciki zargin.
Wadda ta yi zargin ta shaida wa kwamitin cewa a shirye take ta ba da duk bayanan da ake bukata duk lokacin da aka bukaci ta yi haka kuma a ko’ina ne.
Yanzu dai kwamitin ya zabi mako mai zuwa domin zaman gudanar da bincike a kan wannan zargi.
Da farko Shugaban Kwamitin, dan Jam’iyyar Republican ya ba da shawarar a yi wannan tattaunawar ta wayar tarho da duk mutanen biyu amma daukacin ’yan kwamitin suka ce sai dai kowannensu ya hallara gaban kwamitin.
Da kuma aka tuntubi Kabanaugh game da wannan batu ya ce ba komai cikin wannan zargi illa zuki ta malle, sannan ya ce a shirye yake ya ba da bayanai a gaban kwamitin da ke tantance shi a duk lokacin da suka bukace shi domin ya tsira da martabarsa. A cewarsa, shi bai da wata masaniya a kan abin da ake zarginsa.
Yanzu dai an kebe ranar Littini mai zuwa a matsayin ranar da mutanen biyu za su bayyana a gaban kwamitin su yi rantsuwa domin bayyana abin da suka sani game da wannan batu.
Da aka tambayi Shugaba Trump ko yana da niyyar sake wani a kan wannan mukami sai ya ce ba zai sake ba kuma yana kan bakarsa, domin ba inda a tarihinsa aka nuna cewa mutumin da ya zaba ya taba aikata wani abin assha musammam irin wannan da ake zarginsa da aikatawa.
Ya ce sanatocin suna dakatar da tantancewar ce kawai domin su dadada wa kansu kurum, wannan kuma ba laifi ba ne.
Kuma da wani dan jarida ya tambaye shi ko shi Kabanaugh ya fada masa cewa zai janye daga nada shi a kan wannan mukami saboda alakanta shi da wannan batu? Sai Shugaba Trump ya ce wa dan jaridar “Wannan batun banza kake yi.”
Wadansu sanatoci da ke cikin kwamitin da aka tambaye su ra’ayoyinsu game da matsayin mutumin da ke gabansu domin tantancewa, sai Sanata Jeff Flake na Jam’iyyar Republican ya ce ba ma shi ba, babu wani dan kwamiti da zai tantance Kabanugh ba tare da ya ji daga bangaren wannan matar ba. Shi ma Sanata Lindsey Graham na Jam’iyyar Republican cewa ya yi yana maraba da bayyanar Ford domin ta ba da bayani.
Yanzu dai bayan kwamitin ya saurari bahasi daga mutanen biyu zai mika rahoto ga Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) domin ita ma ta gudanar da bincike kafin a dauki matsaya.
An halatta shan wiwi a Afirka ta Kudu
Labarai daga Isiyaku Muhammed
Kotunkoli ta Afirka ta Kudu ta halatta wa mutanen da suka balaga tu’ammuli da tabar wiwi a wuraren taruwar jama’a a kasar.
Masu fafitukar ganin an rika tu’ammuli da tabar wiwi a kasar sun yi ta nuna murnarsu a fili suna masu cewa, “Mun samu kanmu yanzu,” bayan kotu ta yanke hukuncin wanda ba a taba yin irinsa ba kuma ba a zata ba.
Dukan alkalan kotun sun kuma amince mutane su rika noman tabar wiwi domin su rika sha kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi adawa da halatta shan wiwi, tana mai cewa shan wiwi yana da “illa” ga lafiyar jama’a.
Har yanzu ba ta yi tsokaci kan wannan hukunci ba.
A watan Afrilu, Zimbabwe ta zama kasa biyu a Afirka, baya ga Lesotho da ta halatta yin tu’ammali da wiwi a matsayin magani.
Wadansu mutanen kasar Afirka ta Kudu uku ne da ake tuhuma da shan wiwi ne suka kai kara kotu, suna cewa haramta shan wiwin ya tauye hakkinsu na walwala.