Zargin juyin mulki: DSS ta kama mutum 5 na hannun daman Sylva
Sylva ya yi ɓatan-dabo tun da ya shiga ɓuya, lamarin da ya sa jami’an tsaro ke nemansa ruwa a jallo.
Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta kama mutum biyar waɗanda na hannun daman Tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur ne, Timipre Sylva.
An ce an kama mutanen ne saboda zargin sun ɓoye bayanai kan inda Sylva yake.
- An horar da manoman tumatir 100 kan dabarun rage tasirin sauyin yanayi
- DSS ta kama tsohon ministan Tinubu, Uche Nnaji
Sylva ya ɓuya tun bayan da aka zarge da hannu a yunƙuri yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.
Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara mai ƙunshe da tuhume-tuhume 13 a kan mutum bakwai da ake zargi da shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa, haɗa baki domin kifar da gwamnati, laifukan da suka shafi ta’addanci da kuma sauran laifukan da suka shafi barazana ga tsaron ƙasa.
Sylva, wanda tsohon gwamnan Jihar Bayelsa ne, na daga cikin mutum bakwai da ake nema ruwa a jallo tun watan Afrilu.
Ana ci gaba da shari’arsa a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ba tare da ya halarta ba.
Sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana (mai ritaya), Kyaftin Victor Erasmus Ochegobia (mai ritaya), Sufeto Ahmed Ibrahim na rundunar ’yan sanda, Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani.
Haka kuma, akwai wasu jami’an soji da ke fuskantar shari’ar a kotun soji kan wannan lamari.
Wata babbar majiya a fannin tsaro, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce an yi wa mutum biyar da aka kama tambayoyi, kuma nan gaba za a gurfanar da su a kotu.
Majiyar ta ce ana zargin sun ƙi sanar da jami’ai inda Sylva yake, tare da ɓoye wasu bayanan da za su taimaka wajen kama shi.
“Sun ƙi bai wa jami’ai haɗin kai. Wannan na nufin su ma suna da hannu a lamari kuma ya saɓa wa dimokuraɗiyya.
“Nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da a gaban kotu,” in ji majiyar