Zargin karkatar da hatsi: Gwamnan Kano ya dakatar da shugaban kamfanin KASCO

An dakatar da shugaban ne kan zargin karkatar da hatsi.

Zargin karkatar da hatsi: Gwamnan Kano ya dakatar da shugaban kamfanin KASCO

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayar da umarnin dakatar da Daraktan Kamfanin Samar da Takin Zamani na Jihar (KASCO), Dokta Tukur Dayyabu Minjibir.

Ana zargin dakataccen shugaban kamfanin ne da karkatar da wani hatsi mallakin gwamnati.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Baffa Abdullahi Bichi, ne ya sanar da dakatarwar ranar Laraba, inda ya danganta faruwar lamarin da rashin da’a.

Bichi ya mika umarnin Gwamna Abba ne a wata wasika mai dauke da kwanan wata 12 ga watan Satumban 2023.

Ya ce, “An dakatar da Daraktan ne bisa zarginsa da hannu a sayar da hatsin da bai dace ba na Gwamnatin Jihar Kano.

”An umurci Dayyabu da ya mika al’amuran kamfanin ga babban jami’in kamfanin nan take har sai an kammala bincike,” in ji sanarwar.

Aminiya ta rawaito cewa a kwanakin baya ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta maka tsohon manajan kamfanin KASCO, Bala Mohammed da wasu mutum hudu a gaban kotu bisa zargin karkatar da kayayyakin amfanin gona na Naira biliyan hudu.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo