Zargin kashe yarinya: An kone wani fasto a Kankiya
A ranar Talatar da ta gabata ce mutanen da suka fusata suka kashe wani fasto mai kimanin shekara 50 a karamar Hukumar Kankiya biza zarginsa da kashe wata yarinya.Faston mai suna Dike Ocha na cocin Assembly of God an kai masa farmaki ne bayan da aka gano rubabbiyar gawar wata yarniya ’yar shekara shida a […]
A ranar Talatar da ta gabata ce mutanen da suka fusata suka kashe wani fasto mai kimanin shekara 50 a karamar Hukumar Kankiya biza zarginsa da kashe wata yarinya.
Faston mai suna Dike Ocha na cocin Assembly of God an kai masa farmaki ne bayan da aka gano rubabbiyar gawar wata yarniya ’yar shekara shida a kusa da gidansa.
Yarinyar mai suna Fatima Yusuf Yaro, ta bace ne kwanaki hudu baya a kauyensu Mashasha da ke yankin Kankiya kamar yadda Aminiya ta samu labari.
An rika baza jita-jita a garin Kankiya cewa an gano gawar marigayiyar ce a gidan faston wanda ke haya a gidan da aka ce mallakar wani tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Katsina ne da ke rukunin gidaje masu sauki kudi a Kankiya.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa,”Lokacin da aka shiga gidan faston an rika jin wari, kuma sai aka ga gawar yarinyar a cikin wani daki an cire matuncinta da wasu sassan jikinta.”
Majiyarmu ta ce ganin haka ne ya sa jama’a suka harzuka suka fara dukansa kafin jami’an tsaro su kwace shi don kai shi asibiti, amma jama’a suka ci karfinsu, suka kashe shi suka kone gawarsa a kusa da asibitin.
Shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar ta Kankiya Alhaji Abubakar Lawal da Hakimin Kankiya kuma Kankiyan Katsina Alhaji Sada da jami’an ne suka yi kokarin kwantar da hankulan jama’a musamman masu kokarin danganta al’amarin da addini, wadanda suka kone wani coci da ke Sabuwar Abuja.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Alhaji Mohammed Wurdi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe faston, ya ce lamarin ba ya da alaka da addini, illa wani aiki ne na mutane marasa tunani a cikin al’umma. Daga Ahmad Kabir, Katsina
A ranar Talatar da ta gabata ce mutanen da suka fusata suka kashe wani fasto mai kimanin shekara 50 a karamar Hukumar Kankiya biza zarginsa da kashe wata yarinya.
Faston mai suna Dike Ocha na cocin Assembly of God an kai masa farmaki ne bayan da aka gano rubabbiyar gawar wata yarniya ’yar shekara shida a kusa da gidansa.
Yarinyar mai suna Fatima Yusuf Yaro, ta bace ne kwanaki hudu baya a kauyensu Mashasha da ke yankin Kankiya kamar yadda Aminiya ta samu labari.
An rika baza jita-jita a garin Kankiya cewa an gano gawar marigayiyar ce a gidan faston wanda ke haya a gidan da aka ce mallakar wani tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Katsina ne da ke rukunin gidaje masu sauki kudi a Kankiya.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa,”Lokacin da aka shiga gidan faston an rika jin wari, kuma sai aka ga gawar yarinyar a cikin wani daki an cire matuncinta da wasu sassan jikinta.”
Majiyarmu ta ce ganin haka ne ya sa jama’a suka harzuka suka fara dukansa kafin jami’an tsaro su kwace shi don kai shi asibiti, amma jama’a suka ci karfinsu, suka kashe shi suka kone gawarsa a kusa da asibitin.
Shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar ta Kankiya Alhaji Abubakar Lawal da Hakimin Kankiya kuma Kankiyan Katsina Alhaji Sada da jami’an ne suka yi kokarin kwantar da hankulan jama’a musamman masu kokarin danganta al’amarin da addini, wadanda suka kone wani coci da ke Sabuwar Abuja.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Alhaji Mohammed Wurdi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe faston, ya ce lamarin ba ya da alaka da addini, illa wani aiki ne na mutane marasa tunani a cikin al’umma.