Zargin kisa: Ana bincike kan rasuwar Kwamishinan ’yan sanda a Borno

’Yan sandan sun fara bincike kan rasuwar Kwamishinan ’Yan Sandan Mai Kula da Sauya Tunanin ’Yan Ta’adda Ibrahim Idriss Garba

Zargin kisa: Ana bincike kan rasuwar Kwamishinan ’yan sanda a Borno

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

’Yan sandan sun fara bincike kan kisan gilla a dake zargin an yi wa Kwamishinan ’Yan Sandan Mai Kula da Sauya Tunanin ’Yan Ta’adda da kuma Sake Tsuguanr da Al’umma (RRR) na jihar Ibrahim Idriss Garba.

A safiyar Asabar Idriss Garba ya rasu a gidansa da ke Rukunin Gidajen 777 da ke Maiduguri, babban birnin jihar, aka kuma yi masa jana’iza bisa tsarin addinin Islama.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da musabbabin rasuwar tasa, amma wasu majiyoyi na danganta lamarin da ciwon zuciya, wasu kuma na zargin guba ce ta yi ajalinsa.

Rasuwar tasa ta zo ne kimanin wata guda bayan ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a cikin ayarin Gamnan Babagana Zulum a lokacin da yake rangadi a yankin Kudancin jihar.

A sakon ta’aziyyar Gwamna Babagana Zulum, kakakinsa, Isa Gusau ya ce ’yan sanda sun fara bincike kan rasuwar kwamishinan ’yan sandan, wanda tsohon mashawarcin gwamnan ne a kan ayyuka na musamman, kafin a yi masa karin girma zuwa kwamishina.

Injinia Idriss Gaba ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar da kuma mahaifinsa.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS