Zargin Kisa: ’Yan sandan Kano sun gabatar da bayanan tuhumar Doguwa

Ana zargin Doguwa da daukar nauyin tada zaune-tsaye a lokacin zaben ranar 26 ga watan Fabrairu.

Zargin Kisa: ’Yan sandan Kano sun gabatar da bayanan tuhumar Doguwa

Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta mika wa ma’aikatar shari’a ta jihar rahoton zargin kisa da ake zargin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da aikatawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa a ranar Juma’a, jim kadan bayan ya karbi takardar bayanan, babban lauyan ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya mika takardar ga ma’aikatar da misalin karfe 12:45 na ranar Juma’a.

“Ina so na tabbatar wa jama’a cewa nan ba da jimawa ba, za mu yi nazarin shari’ar”.

Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan Shari’ar jihar ya sanar cewa ma’aikatar ta mayar da rahoton ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike, inda ta nemi karin bayani kan zargin da ake yi wa Dogwa don gurfanar da Doguwa.

Daga cikin bayanan da ma’aikatar ta nema har da hoton gawarwakin da aka kashe da bayanan shaidu da bindigar da aka kwato da sauran abubuwan ake zargin an yi amfani da su wajen ainata laifukan.

Rundunar ‘an Sandan Jihar Kano ta kama Doguwa tare da gurfanar da shi tare da wasu bisa laifin hada baki da kuma kisan kai, wanda ya saba wa sashe na 97, 114, 221,247 da 336 na kundin final kod.

Dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa Doguwa ya aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu a Karamar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.