Zargin kisan kare dangi: Turkiyya ta gayyaci jakadan batican
kasar Turkiyya ta gayyaci Jakadan fadar Fafaroma ta batican da ke kasar, domin ya yi mata bayani kan manufar kalaman Fafaroma Francis da ke ikirarin kisan kiyashi aka yi wa Armeniyawa, a hannun dakarun Daular Usmaniyya lokacin Yakin Duniya na Farko. Babu dai bayanai game da abubuwan da ake bukatar sani daga Jakadan amma Ma’aikatar […]
kasar Turkiyya ta gayyaci Jakadan fadar Fafaroma ta batican da ke kasar, domin ya yi mata bayani kan manufar kalaman Fafaroma Francis da ke ikirarin kisan kiyashi aka yi wa Armeniyawa, a hannun dakarun Daular Usmaniyya lokacin Yakin Duniya na Farko.
Babu dai bayanai game da abubuwan da ake bukatar sani daga Jakadan amma Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce nan gaba za a fitar da sanarwa kan lamarin.
kasar Turkiyya ta sha nuna rashin amincewa da kalaman kisan kiyashi, da ake cewa an yi wa Armeniyawa a Yakin Duniya na Farko.
Turkiyya ta sha nanata kin amincewatra da daukar laifin kisan kare dangin da ake cewa an yi wa Ameniyawa a lokacin yakin shekara 100 da suka wuce.
kasashen duniya dai na ta matsin lamba ga gwamnatin Turkiyya da suke zargin ta da kisan kare dangi ga Armeniya a lokacin Yakin duniya na Farko, kan ta amince da wannan zargi.
Dakarun Daular Usmaniyya sun fafata da daular Rasha, sai dai Turkiyya ta tsaya kan bakanta cewa ba za ta karbi laifin da ake kokarin kakaba mata ba.
Turkiya ta ki amincewa da karbar laifin ne inda ta mayar da martani ga Fafaroma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika ta duniya dangane da kalmar “Kisan kare dangi” da yake amfani da ita wajen siffanta aukuwar lamarin
Firayi Ministan Turkiya Ahmed Dabutoglu, a martanin da ya mayar ga Fafaroman, ya caccake shi da cewa yana bin bayan bangare daya ne a lamarin, kuma ya ce bai nuna damuwarsa ba a kan halin da Musulmi suka shiga a lokacin barkewar Yakin Duniya na Farkon ba.
Gwamnatin Turkiyya dai ta bayyana cewa, dubban Turkawa da Armeniyawa ne suka rasa rayukansu a yakin da dakarun Daular Usamaniyya suka fafata da daular Rasha wadda ta yi kokarin karbe iko da yankin Anatoliya a wancan lokacin.