Zargin kunar bakin wake: Wadda aka kashe a Bauchi mai tabin hankali ce – Mahaifiyarta

A ranar Lahadin da ta gabata ne wadansu matasa suka kashe wata mata a Bauchi lokacin da nemi shiga garejin Muda Lawan amma ta ki yarda a caje ta, lamarin da ya sanya matasan suke zargin tana dauke da bam ne, daga karshe dai suka kashe ta suka kona gawarta. Daga bisani ne aka gano […]

Zargin kunar bakin wake: Wadda aka kashe a Bauchi mai tabin hankali ce – Mahaifiyarta

A ranar Lahadin da ta gabata ne wadansu matasa suka kashe wata mata a Bauchi lokacin da nemi shiga garejin Muda Lawan amma ta ki yarda a caje ta, lamarin da ya sanya matasan suke zargin tana dauke da bam ne, daga karshe dai suka kashe ta suka kona gawarta. Daga bisani ne aka gano cewa ba ‘yar kunar bakin wake ba ce, hasali ma dai tana fama da tabin hankali ne, kamar yadda mahaifiyarta ta tabbatar wa Aminiya a wannan hirar da ta yi da ita.

Aminiya: Da farko za mu so ki gabatar da kanki?
Sunana Madam Rahap Haruna, mahaifiyar Tabita wacce aka yi mata kisan gilla a kasuwar ‘yan doya da ke Muda Lawan a Bauchi. Ina da ‘ya’ya shida, kuma ita ce babbar ‘yata, duk ‘ya’yana babu wanda take tallafa min kamarta, saboda haka muna bakin cikin abin da aka yi mata. Daga lokaci zuwa lokaci ne ciwo yake tashi mata, idan ya tashi sai ta fita daga gida babu wanda ya san ina ta shiga.
Aminiya: Yushe mahaifinta ya rasu?
Mahaifinta ya rasu a ranar 7 ga watan Mayu shekarar 2014, kuma tun lokacin yana duniya take fama da ciwon tabin hankali.
Aminiya: Yaushe kika samu labarin rasuwarta?
Ranar Lahadi muka samu labari bayan da muka fito daga coci sai labari ya zo mana na abin da aka yi mata. An samun katin shaida (ID CARD) na kanwanta daga nan ne ‘yan sanda suka zo suka ba mu labarin abin da ya faru.

Aminiya: Me kike so a yi idan an cafko wadanda suka yi mata kisan gillar?

Abin da nake so a yi wa wadanda suka kashe min ‘yata shi ne, a yi musu hukunci daidai da abin da suka aikata, mutumin da yake da imani babu inda zai sa taya ya kona mutum saboda zargin cewa ya ki tsayawa a caje shi. Ina kira da babban murya ga gwamnati da ta bi mana hakkinmu, domin matukar aka yi shiru da maganar kamar an bude kofa ne ga mutane su cigaba da kashe al’umma a jihar Bauchi.
Har zuwa lokacin da muke wannan tattaunawa da kai babu wani daga cikin jami’an gwamnatin Malam Isa Yuguda da suka mana ta’aziyyar rasuwar Tabita, ko da ta kafofin watsa labarai ne. Shiru kake ji kamar an shuka dusa. Muna matukar godiya ga wadansu daga cikin ‘yan jarida a Bauchi bisa yadda suke cigaba da bin diddigin wannan labari na kisan Tabita.
Aminiya: Idan ba a samu wadanda suka aikata kisan ba wane mataki za ku dauka?
Maganar gaskiya ita ce dole a nemo wadanda suka aikata kisan, wannan ita ce magana ta gaskiya da zan iya fada maka. Bayan haka, wannan yarinya ta kware sosai wajen dinkin keke, domin tun tana karama take min hidima a matsayina na mahaifiyarta. Kuma babu abin da aka samu a jikinta balle a ce tana dauke da bama-bamai, wadanda suke wajen sun tabbatar da haka, rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta tabbatar da haka ga manema labarai.
Aminiya: Daga karshe mene ne sakonki?
Babban sakona shi ne, ya kamata al’umma su san abin da suke yi, bai kamata a rika kashe mutanen da suke da rashin lafiya a kansu ba.