Zargin Kwartanci: Allah Zai bi min haƙƙina a lahira — Wanda yake ƙara
Mijin matar ya ce ko da kotu ta wanke waɗanda yake zargin Allah zai saka masa cin amanar da aka masa.
Nasiru Buba, wanda ya zargi Kwamishinan Ma’aikatar Harkoki na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, da aikata zina da matarsa, ya yi watsi da hukuncin da kotun shari’ar Musulunci ta yanke na wanke kwamishinan.
Idan za a tuna, Aminiya ta ruwaito cewa kotun shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu a Jihar Kano, ta kori ƙarar saboda rashin gamsasshiyar hujja.
- Ciyaman ya naɗa hadimai kan harkokin doya da yalo a Enugu
- Kwalara ta kashe mutum 1 wasu 60 na a asibiti a Filato
Alƙalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya ce binciken ‘yan sanda ya nuna babu wata hujja da ke nuna kwamishinan ya aikata laifin.
“Rahoton bincike daga ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, ya nuna babu wata hujja da ta tabbatar da cewa akwai alaƙa tsakanin Auwal Danladi Sankara da Tasleem Baba Nabegu,” in ji alƙalin.
“Tun da mai ƙara da lauyoyinsa ba su halarci zaman kotu don ƙalubalantar rahoton ’yan sanda, ba ni da zaɓin da ya wuce na yi watsi da ƙarar.”
Amma yayin da yake magana da manema labarai a Kano, Buba ya nuna rashin jin daɗinsa da hukuncin da kotun ta yanke.
Ya ce, ya gabatar da ƙwararan hujjoji ga ’yan sanda, ciki har da hotuna 854, bidiyo sama da 100, sakonnin murya na WhatsApp sama da 200, da kuma naɗar murya sama da 500.
“Yawancin waɗannan hujojji na samo ne daga wajen matata, Tasleem,” in ji Buba.
“Ko da kotu ta wanke su, ba su wanku ba a wajen Allah ko a idon waɗanda suka san gaskiyar al’amarin. Na bar komai a hannun Allah, kuma Shi ne zai yi hukunci, insha Allah.”
Lauyan Buba, Rabi’u Sidi, ya ce ba su samu wata sanarwa ba game da zaman kotun, shi ya sa ba su halarci zaman ba.
“Muna da muhimmanci a wannan ƙara, amma babu wanda ya sanar da mu cewa za a yi zaman kotu.
“Sai kawai muka ji yadda aka yanke hukuncin a labarai,” in ji shi.
Lauyan ya ƙara da cewa tawagar lauyoyinsu za ta zauna don yanke matakin da za su ɗauka na gaba.
Idan za a tuna, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama Kwamishinan a ranar 17 ga watan Agusta, 2024, tare da wata matar aure a wani kango.
Sai dai kwamishinan ya musanta zargin da ake masa.