Zargin kwartanci: Hisbah ta kama kwamishina da matar aure a Jigawa

Hisbah ta kama wani kwamishina bisa zargin sa da lalata da matar aure a Jihar Jigawa

Zargin kwartanci: Hisbah ta kama kwamishina da matar aure a Jigawa

Jami’an Hisbah

Hukumar Hisbah ta kama wani kwamishina bisa zargin sa da lalata da matar aure a Jihar Jigawa.

Kwamishinan da hukumar ba ta bayyana sunansa ba, ya shiga hannu ne bayan ƙarar da mijin matar ya shigar, inda yake zargin matar kuma uwar ’ya’yansa biyu tana lalata da kwamishinan a bayan idonsa.

Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa sun kama kwamishinan da matar ne bayan jami’an Hisbar da mijin matar sun rutsa su a wani kango mallakin kwamishinan a cikin mota.

Ya ce, ganin su ke da wuya, matar ta yi yunƙurin tserewa a motar, inda ta buge mai gadin.

Amma ya bayyana cewa daga bisani rundunar ta samu nasarar tsayar da ita da nasu motocin.

An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Zargin kwartanci: Hisbah ta kama kwamishina da matar aure a Jigawa

Fashewar tankar mai: Mamata sun ƙaru zuwa 170

Alabshin N14m ba ya isa ta —Sanata Kalu