Zargin kwartanci: Kotu ta wanke Kwamishinan Jigawa
Kotun ta ja hankalin Hisbah kan gudanar da bincike kafin gurfanar da mutum a kotu.
Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Ƙofar Kudu a Jihar Kano, ta wanke Kwamishinan Harkoki na Musamman na Jihar Jigawa da ka dakatar, Auwal Danladi Sankara, daga zargin aikata zina da wata matar aure.
Tsohon mijin matar da ake zargi, Nasiru Buba ne, ya kai ƙarar, inda ya zargi Sankara da mu’amala da matarsa, Tasleem Baba Nabegu.
- Gwamnatin Obasanjo ce ta kafa tarihin cin hanci da rashawa mafi muni a Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa
- Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos
A yayin yanke hukuncin, alƙalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya ja hankalin hukumomi kamar Hisbah cewa su riƙa yin bincike mai zurfi kafin su ɗauki mataki, musamman idan zargi ya shafi mutane masu muƙami.
Alƙalin ya bayyana cewa binciken da ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya gudanar, ya nuna cewa babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da ake yi wa Sankara.
“Rahoton ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya nuna babu wata shaida da ke tabbatar da alaƙar zina tsakanin Auwal Danladi Sankara da Tasleem Baba Nabegu,” in ji alƙalin.
Kotun ta kuma lura cewa Nasiru Buba da lauyoyinsa ba su halarci zaman kotun ba don ƙalubalantar sakamakon binciken ’yan sanda.
“Tunda wanda ya shigar da ƙara da lauyoyinsa ba su zo ba don su ƙalubalantar rahoton, ba ni da zaɓi face na yi watsi da ƙarar,” in ji alƙali Sarki Yola.
Lauyan Sankara, Barista Sadam Suleiman, ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotu.
“Tun farko mun tabbatar da cewa wanda muke karewa ba shi da laifi, kuma kotu ta tabbatar da hakan ta hanyar rahoton binciken ’yan sanda.”
A ɓangare guda, Rabiu Shu’aibu, lauya mai kare Tasleem Baba Nabegu, ya bayyana cewa suna duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan Nasiru Buba bisa zargin ɓata mats suna.
“Za mu tattauna da wacce muke karewa kan yiwuwar shigar da Nasiru Buba ƙars saboda ɓata mata suna,” in ji Shu’aibu.