Zargin laifi: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta kaddamar da shirin yin gyara da kuma tantance ’yan banga domin kawar da bata-garin cikin

Zargin laifi: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

‘Yan Banga (Hoto daga trtworld)

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta kaddamar da shirin yin gyara da kuma tantance ’yan banga domin kawar da bata-gari a cikinsu.

Kwamishin ’yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya sanar da shirin bayan an kama wasu ’yan banga uku da aikata manyan laifuka.

Ya jaddada muhimmancin sake duba ayyukan ’yan banga a jihar, duk da  muhimmiyar rawar da suke takawa wajen taimaka wa jami’an tsaro a yaki da miyagun laifuka.

Ya ce yin gyaran da kuma tantancewa ya zama dole sakamakon korafe-korafen neman yin hakan daga jama’a.

Ya bayyana cewa jama’a sun yi kiran ne bayan kama wasu ’yan banga uku da laifin hada baki wajen shiga gida, sata, kwace da kuma sayar da kayan sata a Damaturu.

Wata sanarwa da DSP Dungus Abdul Karim, kakakin rundunar, ya fitar, ta ce wasu daga cikin ’yan banga sun kai korafi bayan faruwar lamarin.

“A ranar 27 ga watan Yuni, 2024, rundunar ta amsa kiran wani mai shago a Damaturu, wanda ya dauki ’yan banga aikin gadi, amma suka kwashe kayan shagon na makudan kudade ba tare da bayani ba.

“Bincike ya kai ga kama wasu mutane biyu da kayan sata da ake zargin sun saya ne daga wani dan banga wanda nan take aka kama shi.

“Ana shawarta jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen daukar masu gadi, sannan su kai rahoton ’yan banga da aka ga suna aikata laifi a bakin aikinsu.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, rundunar tana ɓullo da tsare-tsare don daukar bayanan ’yan banga domin sa ido kan ayyukansu.

Ta ci gaba da cewa ofisoshin ’yan sanda na yankuna da ke jihar za su jagoranci wannan aikin tantancewan domin kawar da baragurbi a cikin ’yan banga. kwamishinan.

“Don  haka ake kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa ’yan sanda wajen jainrahoton ayyukan jami’an tsaron da ba su dace ba a hedkwatar jihar ta lamba 07068858500, ko kuma a gabatar da wasikar korafin ga kwamishinan ’yan sanda  ta hanyar kakakin rundunar,” in ji sanarwar.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya