Zargin N37bn: Yadda Sadiya Umar-Farouq ta kwana a hannun EFCC
Tsohuwar ministar jinkai, Sadiya Umar-Farouq ta kwana a ofishin Hukumar EFCC, inda ka titsiye ta kan badaƙalar Naira biliyan 37.
Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar-Farouq ta kwana a ofishin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), inda aka titsiye ta, kan badaƙalar Naira biliyan 37.
A daren Lainin Wani jami’in EFCC da ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da izinin yin magana a hukumance ya ce tsohuwar ministar, wadda suka shafe sa’o’i suma mata tambayoyi za ta kwana ofishin hukumar ne domin ta ba da karin cikakkun bayanai da suka dace kan badaƙalar.
Ya ce, “Tana ba hukumar hadin kai a binciken inda take ba mu bayanan da suka dace,” inda take yin karin haske bayanan da ke cikin wasu takardu da ke hannun hukumar da kuma wadanda ta zo da su kamar yadda aka umarce ta.
EFCC ta tistsiye tsohuwar ministar ce kan badaƙalar N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar a karkashin kulawarta ta hannun wani dan kwangila mai suna James Okwete. Sadiya dai ta musanta sanin dan kwangilar ko yin wata hulda da shi.
- Kotu ta umarci Gwamnati ta biya Emefiele diyyar N100m
- EFCC ta gayyaci Betta Edu kan badakalar kudin tallafi
A safiyar Litinin ne safiya Umar-Farouq ta kai kanta ofishin hukumar bayan rashin lafiya ya hana ta samun amsa gayyatar hukumar na ranar Larabar da ta gabata.
A makon jiya ne EFCC ta ga gayyaci tsohuwar ministar bayan wani bincike da hukumar ta kaddamar kan ayyukanta a ma’aikatar.
Kokarin wakilinmu na yin magana da kakakin hukumar, Dele Oyewale bai samuu ba, saboda kiran da aka yi wa wayar jami’in bai shiga ba, sannan har yanzu bai a amsa sakon tes da aka aika masa ba.