Zargin N432bn: El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu

El-Rufai ya shigar da kara yana kalubalantar rahoton kwamitin binciken majalisar kan zargin sa da almundahanar biliyan N432

Zargin N432bn: El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar dokokin jihar a kotu kan zargin da take masa na karkatar da Naira biliyan 432 a lokacin mulkinsa.

Majalisar dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufai ta shekarar takwas (2015-2023) da sace Naira biliyan 432 sannan ta bar wa gwamnati mai ci tari bashi.

A ranar Laraba El-Rufai ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta hannun lauyansa, Abdulhakeem Mustapha, inda yake kalubalantar rahoton kwamitin binciken da majalisar ta kafa kan zargin almundahanar.

Karin bayani na tafe

 

 

 

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato