Zargin N82bn: EFCC ta kasa gurfanar da Yahaya Bello a kotu
Hukumar EFCC ta gaza gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello kan sabon zargin badaƙalar Naira biliyan 82
An kasa gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello kan sabon zargin badaƙalar Naira biliyan 82.
Hukumar yaki da almundahana ta EFCC ta kasa gabatar da Yahaya Bello a kotu ranar Alhamis domin kan sabbin tuhume-tuhume 19 kan badaƙalar kuɗaɗe.
Hakan na zuwa ne bayan da farko a ranar Laraba wata Babbar Kotun Abuaj Abuja ta tsare shi, bayan an gurfanar da shi kan badaƙalar karkatar da Naira biliyan 110.4 a lokacin da yake jagorantar Jihar Kogi.
Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kasa gurfanar da tsohon gwamnan ne saboda rashin wasu takardu.
A ranar 30 ga watan Oktoba, alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ayyana 21 ga watan Janairun 2025 a matsayin ranar ya ke hukunci kan gurfanarwar da kuma buƙatar ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ƙoli.
Shari’ar Yahaya Bello dai ta sha fama da samun tsaiko da ɗage zama saboda rashinsa a kotu.