Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
Gwamnatin Kano, ta bayyana kudirinta na bincikar Ganduje da wasu kan zargin aikata badaƙala.
Shugabancin Jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, ya dakatar da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, kan zargin aikata rashawa da gwamnatin jihar ke masa.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa jami’yyar shawara kan harkokin shari’a, Malam Haladu Gwanja Ganduje ya fitar, a ranar Litinin.
- Daliban Chibok 21 sun dawo gida da ’ya’yan Boko Haram 34 —Rahoto
- Mutum 3 sun rasu an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe
Ya ce jami’yyar ta ɗauki matakin ne domin kare martabarta.
Ganduje ya bar wa Kano abun kunya – Abba
Idan za a tuna Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dole ne gwamnatinsa ta binciki tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya zarge shi da bar wa jihar abun kunya.
Ya ce mulkin Ganduje na shekara takwas babu abin da ya haifar face almundahana, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da sayar da kadarorin jihar.
Gwamnan, ya ƙara da cewar wa’adin Ganduje biyu a matsayin gwamna bai taɓuka komai ba sai wawure dukiyar al’umma, zubar da jini wanda ya bar iyalan mutane cikin ƙunci.
Gwamnan, ya ce duk wani mutum da zai hana a binciki Ganduje da iyalansa kan irin badaƙalar da suka yi a Kano, ba cikakken mai kishin jihar ba ne.
Kotu ta sanya ranar gurfanar da Ganduje
Tuni wata babbar Kotu a Kano ta sanya 17 ga watan Afrilun 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.
A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da kuma Lesage General Enterprises.