Zargin rashin lafiyar Atiku ya bar baya da kura

Tsohon Minista, Femi Fani-Kayode, ya yi zargin an garzaya da Atiku Faransa domin ganin likita

Zargin rashin lafiyar Atiku ya bar baya da kura

Kura ta tashi bisa zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, ya yanke jiki ya fadi a filin jirgin sama a hanyar dawowarsa daga yakin neman zabe a Kaduna.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya yi zargin an garzaya da Atiku zuwa kasar Faransa domin ganin likita, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa cewa, “Atiku ya kamu da rashin lafiya bayan dawowarsa daga taron Kaduna; Ya fara korafin cewa yana jin jiri da tsananin radadi a kansa da sassan jikinsa, a tsawon tafiyarsu a jirgi zuwa Abuja.

“Bayan saukarsu a filin jirgin Abuja, ya yanke jiki, aka garzaya da shi zuwa birnin Paris na kasar Fasarsa domin ganin likita. Allah Ya kare shi.”

Femi Fani-Kayode, wanda dan Jam’iyyar APC mai mulki ne, ya ci gaba da cewa, “Amma domin kawar da hankalin jama’a sai washegari da safe suka dauki hotonsa tare da wasu mutane a Paris suka wallafa. To kar ku yarda su mayar da ku wawaye.

“Dan takarar shugaban kasa na PDP na da matsalar rashin lafiya, amma ba su so ’yan Najeriya su sani.”

FFK ya janyo ce-ce-ku-ce a Twitter

Sakon nasa dai ya jawo ce-ce-ku-ce, inda masu mayar da martani ke ta tofa albarcinsu, wasu na caccakar sa, wasu kuma na mawahawa.

Mutum sama da 1,500 ne suka yi tsokaci a kan sakon na Fani-Kayode, wasu sama da 1,00o kuma suka tura sakon, zuwa lokacin da muke rubuta wannan labari.

Da take martani kan sakon na Femi Fani-Kayode, @mode_bolanle, ta ce, “Yanzu ku dubi abin da …. Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya mayar da kansa.”

Shi kuma, @FejiroDaniel1, ya ce, “Na tsani yadda aka siyasantar da batun lafiyar mutane, an ce Tinubu, yanzu kuma Atiku. 

“Kowa na rashin lafiya, hatta injuna na lalacewa a gyara. Ya kamata mu mayar da hankali kan abubuwan da suka fi muhimmanci.”

@izziyidee, ya ce, “Gaskiyar magana ita ce, mutanen nan (’yan siyasa) na matsa wa kansu fiye da yadda ake tunani, shi ya sa ba zan yi mamaki ko in yi wa waninsu dariya don ba shi da lafiya ba.”

A nasa tsokacin, @adurojadgreat, wanda da alama mai goyon bayan dan talarar LP, Peter Obi ne, ya ce, “Aikin ceto Najeriya na bukatar mutum mai koshin lafiya da kaifin basira, ….ba kamar yadda Buhari ya yi wa’adin mulki biyu yana kula da lafiyarsa ba, amma kana ganin ba wata matsala ba ce.

A nan ne, @FejiroDaniel1, ya mayar masa da martani da cewa, “Shi ya sa ake da zabi, idan kana ganin wani dan takara ba shi da koshin lafiya, sai ka nemi mai koshin lafiya ka zaba.

“Ya kamata ka daina matsa wa kanka game da abin da ba ka da cikakkiyar masaniya a kai.”

PDP ta karyata Fani-Kayode

Ana cikin haka ne, kakakin Atiku, Paul Ibe, ya fitar da sanarwa cewa dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi bulaguro zuwa Faransa ne domin ganawa da abokan kasuwancinsa.

“Tsohon mataimakin shugaban kasa ya je Faransa tattaunwa da abokan huldar wasu kamfanoninsa da COVID-19 ta kawo musu cikas kamar sauran harkokin duniya,” in ji sanarwar ta Paul Ibe.

Wani mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku, Daniel Bwala, ya wallafa hoton Atiku a Twitter da cewa, “Yana ganawa da kafofin yada labarai na kasashen waje” a birnin Faris na kasar Faransa ranar Talata, 18 ga Oktobe, 2022.

“Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar PDP tare da ’yan rakiyarsa a Farsana, yana ganawa da ’yan jarida.”

Batun koshin lafiyar ’yan takara shugaban kasa dai na daga cikin abubuwan da ake yawan magana a kai a zaben 2023 da ke tafe, tun bayan da aka yi zargin cewa dan takarar APC, Bola Tinubu ba shi da cikakkiyar lafiya.