Zargin satar jariri ya haifar da takaddama tsakanin asibiti da iyaye

Wasu iyayae da ke zaune a Unguwar Magume a Zariya sun zargi wani asibiti mai zaman kansa da sace jaririnsu. Ma auratan masu suna Mashi-nowa Kolawole da matarsa Amina Osineye sun bayyana wa wa wakilinmu cewa Amina ta haifi tagwaye asibitin da take zuwa awo mai suna St. Luke’s Anglica Hospital Wusasa, a yankin Zariya, […]

Zargin satar jariri ya haifar da takaddama tsakanin asibiti da iyaye
Zargin satar jariri ya haifar da takaddama tsakanin asibiti da iyaye

Wasu iyayae da ke zaune a Unguwar Magume a Zariya sun zargi wani asibiti mai zaman kansa da sace jaririnsu.

Ma auratan masu suna Mashi-nowa Kolawole da matarsa Amina Osineye sun bayyana wa wa wakilinmu cewa Amina ta haifi tagwaye asibitin da take zuwa awo mai suna St. Luke’s Anglica Hospital Wusasa, a yankin Zariya, Jihar Kaduna, amma sai likitocin asibitin suka ce daya ta haifa.
Mista Kolawole ya ce tun lokacin da ya baro Legas ya dawo Zariya shekara hudu da suka wuce, asibitin shi da iyalansu suke zuwa, don haka ko da matarsa ta samu juna nan take zuwa awo, kuma duk binciken da aka yi mata ya nuna cewa cikin da take dauke da shi ’yan biyu ne.
Ya ce, bayan binciken da asibitin ya yi, sun tura matarsa wani asibiti mai zaman kansa mai suna Alheri Medical Imaging & Clinical Serbice da ke lamba 15-18 a Layin Turunku daura da bankin SKY da ke Park Road PZ, Zariya.
Ya ce hoton da ta yi a ranar 9/4/2015, ya kara tabbatar da cewa tagwaye take dauke da su ’yan mako 29, amma da lokacin haihuwa ya yi sai likitocin suka ce aiki za a yi mata.
Mista Kolawole ya ce “Su kansu likitocin asibitin a gwajin da suka yi kafin su yi mata aiki a ranar 14/6/2015 ya kara tabbatar musu da cewa matata tagwaye take dauke da su, bayan an dauke ta zuwa dakin aiki, ina kofar dakin domin jiran sakamakon abin da zai faru zuwa can sai daya daga cikin wadanda suke mata fida ya fito ya ce matata da daya ta haifa ba biyu kamar yadda ake tsammani ba, amma idan ban yarda ba in shigo dakin tiyatar don in gani kafin su rufe cikinta domin dayan ruwa ne ba da ba. Ni kuma na ce ba zan iya shigowa in ga matata a wannan halin ba, amma wanda aka samu mace ce ko na miji domin hoton da ta yi a baya ya nuna cewa tagwayen mace da namiji ne, sai suka ce namiji aka samu. Bayan kamar minti 30, sai kuma na ga an fito min da ’ya mace. Hakan ya haifar min da wasi-wasi a zuciya daga nan sai na ga wani mutum ya zo ya shiga dakin tiyatar suna tattaunawa kafin ya ce masa za shi dakin baki ya jira shi. Wajen fitowar wancan mutum sai ya kalle ni, ya ce sannu fa, kai ne ake wa matarka aiki? Na ce masa eh, ya wuce abinsa hakan ya kara sanya min zargi a zuciyata cewa akwai wani abin da ke faruwa.”
Ya ce tuna cewa hoton da aka yi har zuwa ranar haihuwarta ya nuna tagwaye za ta haifa mace da namiji da kuma yadda da farko aka ce masa namiji ta haifa sanna aka fito masa da ’ya mace, ya sa ya ce bai yarda ba, su fito masa da daya dansa ko ya yi kararsu. “Daga nan takaddama ta kaure a tsakaninmu kasancewar haka kudin da suka caje ni na yi mata aiki Naira dubu 120 ba su karbi ko Naira 100 ba, kokarinsu in bar asibitin don haka na yi kararsu ga ’yan sanda kuma na sanar da manema labari domin gwamnati ta sani tai taimaka min.
Da Aminiya ta nemi jin ta bakin hukumomin asibitin, sakatariyar asibitin ta ce wadanda ya kamata su yi magana suna bakin aiki, inda ta bukaci wakilinmu ya bar lambar wayarsa in sun kammala za a kira shi, amma har lokacin hada wannan rahoto ba su kira ba.
A babban ofishin ’yan sanda na Area Command, Zariya, shugaban ’yan sandan yankin ya tabbatar da kai karar gabansa, amma saboda lamarin na bukatar dogon bincike ya tura su hedkwatarsu da ke Kaduna.