Zargin satar shanu: ’Yan sanda sun harbi jagoran ’yan banga sun kama yaransa takwas
’Yan sanda a yankin Bwari na Birnin Tarayya Abuja na ci gaba da bincike a kan wadansu ’yan banga da suka je yankin daga Jihar Nassarawa da nufin kubutar da wasu shanu, bayan da ’yan sandan suka yi artabu d ’yan bangan su tara da suka je daga kauyen Saka a karamar Hukumar Karu ta […]
’Yan sanda a yankin Bwari na Birnin Tarayya Abuja na ci gaba da bincike a kan wadansu ’yan banga da suka je yankin daga Jihar Nassarawa da nufin kubutar da wasu shanu, bayan da ’yan sandan suka yi artabu d ’yan bangan su tara da suka je daga kauyen Saka a karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa don rakiya ga wasu Fulani da shanunsu.
daya daga cikin ’yan bangan mai suna Jamilu Isa ya shaida wa Aminiya sun je yankin ne bisa gayyatar wani makiyayi da ke son hijira da shanunsa sama da 50, saboda addabarsa da barayi suka yi a Bwari, har ta kai sun yi garkuwa da matarsa na kwana biyar kafin su ka sako ta a makon jiya.
dan bangar wanda ke jinyar jagoransu da kwance a Babban Asibitin Bwari bayan ’yan sanda sun harbe shi bisa zargin barayin shanu ne, ya ce bayan barayin sun sako matar Bafulatanin sun bukaci ya ajiye musu Naira miliyan uku za su zo su karba, ko ya gamu da fushinsu. Ya ce kafin zuwansu yankin sun samu takarda daga ofishin ’yan sanda na yanki a Jihar Nasarawa a rubuce da ke bayyana abin da za su yi, amma sai ’yan sanda suka far musu a daidai lokacin da suka fara rakiyar a ranar Asabar, inda suka harbi jagoransu a kafa sannan suka tsare sauran a ofishinsu.
Wani dan sanda da ke gadin majinyacin a asibitin na Bwari da ya katse hirar, ya bayyana wa wakilinmu cewa sun samu kira ta waya a ranar daga wajen garin Bwari, inda aka shaida musu cewa wadansu mutane dauke da bindiga da ake zargin barayin shanu ne na wucewa ta yankin, kuma a dalilin haka ne suka far musu suka harbi jagoransu a kafa don karya lagonsu.
Ya ce koda yake ’yan bangan sun gaya musu su ba barayin shanu ba ne, bincike ne kadai zai tabbatar da haka, saboda haka za su ci gaba da tsare su.
Wakilinmu ya je kauyen Saka da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi inda ’yan bangan suka ce sun fito, inda Ardon Fulanin kauyen Malam Fulani Jaffire ya ce tafiyar tasu ta biyo bayan dauki ne da mai shanun ya nema.
Malam Jaffire ya ce jagoran ’yan bangan ya bar garin a ranar Juma’a tare da hudu daga cikin yaransa inda za su hadu da karin wasu ’yan baga shida daga wasu kauyuka biyu. Ya ce motar da suka tafi da ita za ta dauko iyalan mutumin da kayansu, su kuma ’yan bangan su koro shanun zuwa wani wuri da mutumin yake son dawowa saboda yana cike da fargaba.
Shugaban kungiyar Miiyetti Allah ta Jihar Nasarawa Alhaji Gidado Idris ya ce sun ba da kwafin takardar izinin tura ’yan bangan ga ’yan bangan da suka samu daga ofishin ’yan sanda da ke Keffi, kuma ya bayyana mamakinsa a kan harbe kafar jagoran ’yan bangan da ’yan sandan suka yi.