Zargin son rai: Ya kamata Shugaban APC na Yobe ya sauka
Darakta-Janar na qungiyar, Lawan M. Ibrahim, ya zargi shugaban APC da goyon bayan wani ɗan takarar gwamna a fili kafin fara tsarin zaɓen jam’iyyar.
Wata ƙungiya ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar Yobe First Movement ta yi kira da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Gadaka, da ya gaggauta yin murabus bisa zargin amfani da tsarin daidaito maimakon zaɓen fid-da-gwani na ’yan takarar gwamna kamar yadda dokar jam’iyyar ta tsara.
A lokacin wani taron manema labarai a Damaturu, Darakta-Janar na qungiyar, Lawan M. Ibrahim, ya zargi shugaban APC da goyon bayan wani ɗan takarar gwamna a fili kafin fara tsarin zaɓen jam’iyyar.
A cewar ƙungiyar, an ga shugaban jam’iyyar kwanan nan tare da tsohon gwamnan kuma Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Alhaji Ibrahim Geidam da gwamna Mai Mala Buni a wani taron jama’a inda ake zargin sun goyi bayan kuma sun ɗaga hannun wani ɗan takarar gwamna Baba Mallam Wali.
Ta bayyana matakin a matsayin keta haddi, nuna son kai da kuma yinƙurin ƙaƙaba wa ’yan jam’iyyar ɗan takarar da suka fi so a maimakon zaɓen fid-da-gwani na gaskiya domin babban zaɓen 2027.
“Ana sa ran ofishin shugaban jam’iyya na jia ya kasance ne tsayayye a matsayin alƙalin da ba shi da son kai a cikin zaɓukan fid-da-gwaninta na jam’iyyu da kuma na zaɓe maimakon akasin hakan,” in ji Ibrahim.
“Ta hanyar bayyana kansa a fili da wani ɗan takara, hakan yana kawo rashin amincewar membobin jam’iyya game da adalci da daidaiton dimokuraɗiyya na tsarin.”
Don haka ƙungiyar ta yi kira ga shugaban APC na Jihar da ya yi murabus daga muƙaminsa ko kuma ya janye kansa daga duk wani aiki da ya shafi zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar domin dawo da amincewa tsakanin masu neman takara da magoya bayan jam’iyyar.
Ƙungiyar Yobe First Movement ta kuma yi nuni da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya, dokar zaɓe da kundin tsarin mulkin APC, tana mai dagewa cewa dole ne a kare dimokuraɗiyyar cikin gida don tabbatar da zaɓen fid-da-gwani mai gaskiya da sahihanci a jihar.