Zargin Ta’addanci: Kotu ta bayar da umarnin gabatar da shugaban Miyetti Allah
Lauyan Bodejo ya ce tsare shi da aka yi ya saɓa wa dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Babbar Kotun Birnin Tarayya, ta umurci Antoni Janar na Tarayya (AGF) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), su gabatar da Shugaban Miyetti Allah Kautal Kore, Bello Bodejo, a gaban kotu.
Mai Shari’a Mohammed Zubairu ne, ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata.
- ’Yan Najeriya sun kusa yin farin ciki — Remi Tinubu
- Ban yi nadamar cire tallafin man fetur ba – Tinubu
Ya ce a gabatar da Bodejo a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, domin sauraron ƙarar da ta shafi haƙƙinsa na doka.
Lauyan Bodejo, Reuben Atabo (SAN), ya ce tsare Bodejo ya saɓa wa wasu sassa na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da dokokin kotu.
Ya kuma nemi izinin kotu don ƙalubalantar halaccin tsare shi ta hanyar amfani da tsarin doka da ake kira Habeas Corpus.
Rahotanni sun nuna cewa, sojoji sun kama Bodejo ne a ranar 10 ga watan Disamba a ofishinsa da ke Jihar Nasarawa.
An kama shi ne bayan wata hatsaniya da ta ɓarke tsakanin makiyaya da wani tsohon Janar ɗin soja, wanda makiyayan suka ƙwace wa bindiga.
A farkon wannan shekara, DSS ta kama Bodejo bisa zargin ta’addanci, bayan ya kafa wata ƙungiyar tsaro da ya ce manufarta ita ce kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Sai dai an sake shi a watan Mayu bayan Hukumar Binciken Tsaro ta Soji (DIA), ta janye tuhumar da ta shafi kafa ƙungiyar tsaro ta ƙabilanci.
An ce ƙungiyar ta saɓa wa Dokar Hana Ta’addanci ta 2011.