Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai

El-Rufai ya ce da alama “Nuhu na fama da matsanciyar cutar matuwa,” inda ya kara da cewa akwai rubutattun hujjoji da ke tabbatar da kalaman Naja’atu,

Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai

Hajiya Naja’atu Muhammad

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya goyi bayan Hajiya Naja’atu Muhammad a rikicinta da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu.

Rikicin ya kunno kai ne bayan Naja’atu ta bulla a wani bidiyo inda take kushe Nuhu Ribadu ads aiki a gwamantin Tinubu alhali a lokacin da yake Shugaban Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC), ya soki Tinubu da zargin sa da almundahana a yayin taron Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC).

Bayan haka ne Ribadu ta hannun lauyansa Ahmed Raji (SAN), ya bukaci ta janye kalaman nata tare da neman afuwarsa, yana mai barazanar maka ta kotu idan ba ta janye ba, domin kalaman nata na neman zubar masa da kima.

Amma duka da haka, Naja’atu, wadda tsohuwar Kwamishina ce a Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) ta tsaya kai da fata, cewa ba za ta janye ba ballanta na da ba da hakuri.

Ana cikin haka ne, El-Rufai ya bayyana cewa gaskiya ne maganar da Naja’atu game da zargin da Nuhu Ribadu ya yi kan Tinubu gaskiya ne.

El-Rufai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya bayyana cewa yana nan Ribadu ya yi wadannan kalamai a taron FEC, lokacin shi El-Rufai yana Ministan Abuja.

Ya ce da alama “Nuhu na fama da matsanciyar cutar matuwa,” inda ya kara da cewa akwai rubutattun hujjoji da ke tabbatar da kalaman Naja’atu, ciki har da takardun Majalisar Dattawa a shekarar 2006.