Zariya 2019: Jawabin Shugaban Kungiyar Gizagon Najeriya
A ranar Asabar da ta gabata 17-04-1441 (Bayan Hijira), daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) Gizagawan Najeriya suka hallara a zauren taro na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya, Jihar Kaduna, inda suka gudanar da taronsu na bana, wanda shi ne karo na 6 tun kafuwar kungiyar. A bana taron ya samu halartar babban mai […]
A ranar Asabar da ta gabata 17-04-1441 (Bayan Hijira), daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) Gizagawan Najeriya suka hallara a zauren taro na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya, Jihar Kaduna, inda suka gudanar da taronsu na bana, wanda shi ne karo na 6 tun kafuwar kungiyar. A bana taron ya samu halartar babban mai jawabi, Farfesa Ibrahim Malumfashi, na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda ya samu wakilcin Dokta Ibrahim Shehu Liman, shi ma na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda ya gabatar da mukala dangane da “Gudunmawar ’Yan Jarida Ga Rayuwar Al’umma.” Haka kuma an gudanar da addu’o’i da jawabai na musamman, domin tunawa da daya daga cikin iyayen kungiyar, marigayi Malam Mahmoon Baba-Ahmad. Marigayin, kafin rasuwarsa ya kasance shahararren dan jarida, hasali ma daya ne daga cikin marubuta a jaridar Aminiya. Domin tunawa da gudunmawar da Malam Mahmoon ya ba da wajen fadakarwa ga al’umma, GIZAGO (08065576011) ya karanta wasu daga cikin wakokin marigayin a gaban mahalarta taron. Haka kuma, Shugaban Kungiyar Gizagon Najeriya, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe, GZG-023-GMB (08023281167, 08023281167) ya gabatar da jawabinsa, kamar haka:
Masu girma manyan baki, iyayen kungiya a matakan jihohi da kasa, tsofaffin shugabanni a matakan jihohi da kasa, shugabanni masu ci a wannan lokaci, ’yan uwa maza da mata, assalamu alaikum.
Ina godiya ga Allah da Ya sake hada fuskokinmu a wannan rana, a kuma daidai wannan lokaci domin jaddada zumunci.
A irin wannan lokaci ne muke shaukin haduwa da juna cikin annashuwa, ana hira, ana raha, ana dariya, a kuma rabu cikin farin ciki.
Babu shakka wannan shi ne jigon haduwarmu a wannan kungiya mai albarka, wanda ya zamo asalin silar haduwarmu, ta cikin jaridar Aminiya, a shafi na 18; ta dalilin mu’assas Malam Bashir Yahuza Malumfashi. Mun faro wannan tafiya ce, kimanin shekara goma sha daya da suka shude (Afrilu 2008).
Nasarar Haduwarmu:
Alhamdulillah! Ko ba a fada maka ba, ka san an yi hakuri da juna a wurare da dama saboda hakurin ne ya kawo mu ga tsawon wadannan shekaru, haduwarmu ta haifar da nasarori masu dimbin yawa, domin kuwa an hada auratayya a tsakanin mambobi, an kulla alakar kasuwanci, yayin da a gefe guda kuma wasunmu sun kulla zumunci a tsakanin juna, wanda Allah ne Ya san ranar rabuwa. Muna kara addu’a, Allah Ya kara mana zumunci. Hakazalika, a irin wannan haduwar ce Allah Ya hada fuskokinmu da daya daga cikin iyayen wannan kungiya wato, marigayi Malam Mahmoon Baba Ahmad, wanda Allah Ya karbi rayuwarsa, muka kuma shirya wannan taro domin tunawa da shi tare da kara mika ta’aziyyarmu ga ’yan uwa da abokan arziki. Hakika babu abin da wannan kungiya za ta yi ta saka masa ko ta biya shi face addu’o’i da mambobin wannan kungiya suka yi da kuma wadanda za su kara, domin kuwa duk wata shawara da uba kan yi wa dansa, don ganin ya zage ya nemi na kansa, marigayin ya rigaya ya yi mana. Wannan kauna da ke tsakaninmu da shi, ita ce ta sa muka kawo wannan taro mahaifarsa saboda mu kara dankon zumunci da iyalansa.
Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Ya kuma sanya albarka ga zuriyarsa, amin.
Ci gaban da ake samu a kungiya:
Hakika idan muka waiwaya baya daga inda muka karbi ragamar jagorancin wannan kungiya mai albarka, zuwa yanzu zan iya cewa an samu ci gaba, domin kuwa mun yi ayyuka masu tarin yawa cikin yardar Ubangiji. Samun wannan nasara ya biyo bayan irin hadin kai da goyon bayan da muke samu ne daga mambobin wannan kungiya mai albarka. Madalla da Gizagawan Zumunci. Zan iya tunawa, mun dauki alkawurra a lokacin yakin neman zabe, kuma bisa dukkan alamu muna dab da cika alkawurran da izinin Allah.
Alkawuran kuma su ne kamar haka:
a) Maido da ayyukan kungiya a cikin shafin jaridar Aminiya.
b) Hada kan mambobi, ta hanyar kafa kwamitin sulhu.
c) Bude wa uwar kungiya asusun ajiya.
d) Taimakon juna ta hanyar kafa gidauniya.
e) Nema wa kungiya hanyar da za ta dogara da kanta.
f) Kafa kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, wanda muka rantsar da ’yan kwamitin a taronmu na kasa da ya gabata a bara, a Jihar Katsina, kuma muna sa ran nan gaba kadan za mu karbi kundin a Jihar Zamfara, inda za mu bibiyi ayyukan da suka yi; insha Allah.
Kusan dukkan wadancan alkawuran da muka dauka, babu wanda ba mu aiwatar da shi ba, sai wanda na ambata na nema wa kungiya hanyar da za ta dogara da kanta. Tuni shi ma mun gabatar wa mambobi yadda fasalin zai kasance, har ma wadansu sun fara ba da tallafin da zai kai mu ga samun nasara wajen dogaro da kai. Allah Ya saka wa Alhaji Ibrahim Ahmed Katsina da alheri, wanda ya kasance daya daga cikin iyayen wannan kungiya a matakin kasa. A lokacin da muka kai masa ziyara a kwanakin baya, a ofishinsa da ke Abuja, shi ne ya karfafa mana gwiwa, ya kuma dora mu a kan hanya, tare da ba mu shawarwari masu muhimmanci. Ya ce ya ba mu nan da wani lokaci a je a fidda wata gidauniya, duk abin da aka tara a sake tuntubarsa, zai ba mu mafita da za ta kai mu ga hanyar dogaro da kanmu. Shi ne kuma mutum na farko da ya fara sanya nasa tallafi na Naira dubu goma a gidauniyar, sai Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya biyo bayansa da Naira dubu biyar. Daga bisani wadansu daga cin shugabanni da mambobi suka rufa musu baya. Zuwa yanzu dai an tara Naira dubu arba’in da uku da dari biyu. Muna fata ragowar iyayen wannan kungiya mai albarka za su ba da nasu tallafin, domin ganin wannan kungiya ta tsaya da kafafunta wajen dogaro da kai. Hakazalika za mu kara nema wa wannan gidauniya tallafi a cikin wannan dakin taro da ke gudana a halin yanzu. Wani mabaraci da ke rera bakandamiyarsa ya ce: “Babban gida da dadin bara yake, wannan ya ba ka, wannan ya dada maka!” Muna fata mai taro mai sisi ya taimaka. Allah Ya ba da ikon taimakawa, amin.
(Ba nan jawabin ya tsaya ba, amma mun takaita shi nan, saboda rashin wadatar fili).