Zato zunubi ne ko da ya zama hakkun

Tarwatsewar wasu bamabamai da sanyin safiya a babbar tashar mota ta Nyanya da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya kuma yi sanadiyyar asarar rayuka sama da saba’in a tashi guda,  al’amari ne da ya bakanta ran kowane mahalukin kasar nan, kuma hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kasa sauke muhimmin nauyin da ke wuyanta […]

Zato zunubi ne ko da ya zama hakkun
Zato zunubi ne ko da ya zama hakkun

Tarwatsewar wasu bamabamai da sanyin safiya a babbar tashar mota ta Nyanya da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya kuma yi sanadiyyar asarar rayuka sama da saba’in a tashi guda,  al’amari ne da ya bakanta ran kowane mahalukin kasar nan, kuma hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kasa sauke muhimmin nauyin da ke wuyanta na kare rayukan bayin Allah da kuma tsare  dukiyar jama’arta.
Fiye da shekaru hudu ke nan ana ta fama da matsalar rashin tsaro da ake cewa ya samo asali ne saboda rashin adalcin hukumomi wajen tunkarar al’amuran ’yan Boko Haram da ke kukan an kashe masu shugaba, aka kuma takura masu ba bisa dokokin kasa ba, a’a, sai dai don son ran wasu shugabannin da ba su kaunar zaman lafiya. Abu wasa-wasa, sai ga shi nan masifar da wadannan mutanen suka tayar ta yi karfi kamar wutar daji, ta mamaye kusan dukkan sassan shiyyar Arewa-maso-Gabas, kuma a sakamakon rashin tabukawar gwamnatoci wajen dakile illolin da suke haddasawa, sai wasu ’yan ta’addan kuma suka dukufa tayar da rikice-rikicen da suka hana wasu sassan Arewa zaman lumana da kwanciyar hankali.
A yanzu haka, a kullum sai ’yan bindiga sun hallaka dimbin talakawan da ba su ji, ba su kuma gani ba, a shiyyar Arewa-maso-Yamma, sa’annan kuma an kasa gano ko su wane ne ke aikata irin wannan ta’asar, abin sai ka ce babu wata hukuma a kasar. Baicin wadannan kashe-kashen kuma Fulani da sauran manoma suna gamuwa da ta’addancin barayin da ke kore masu garken shanu, walau daga rugagensu ko kuma daga gidajen gonakansu, kuma  yanzu haka ma an haddasa wata gagarumar rigimar da ta janyo wata mummunar fitina ta dambarwa tsakanin manoma da makiyaya a shiyyar Arewa-ta-Tsakiya, inda a can ma a kullum sai an yi asarar rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma wannan wata tsohuwar badakalar ba yau ta kunno kai ba, amma an kasa magance ta, hasali ma kara karfafa ta aka yi don kar a samu zaman lafiya da fahimtar juna.
To amma duk da kokarin da ake ta yi, da kuma sadaukar da kan da mutanen Arewacin kasar nan ke yi don a zauna lafiya, har yanzu ba a daina daukar matakan ingiza wutar da ke neman murkushe yankin ba, domin dukkan abubuwan da ke faruwa gwamnati da manyan jami’anta ba su tausayawa, ko yin takakka zuwa wuraren da bala’o’in ke gawurta don jajantawa. Tun da sun dauka cewa wannan matsala ce ta yankin Arewa, sai a bar ’yan Arewa da ita, idan sun ga dama su yi maganinta, idan kuma suka yi sakaci, sai masu ruruta ta su ci gaba, alabarshi idan Arewar za ta kone kurmus ne sai ta konen, ba abin da zai dada su da kasa.
Sa’ilin da ’yan Najeriya, manya da kananansu, suka dukufa wajen nuna alhinin wannan mugun abin da ya faru a Nyanya, sai ga Shugaba Goodluck Jonathan ya wanke kafa, ya nufi wurin da jaza’in ya auku don gane ma idanunsa irin ta’adin da aka tafka. Amma budar bakinsa ke da wuya bayan isarsa wurin, sai kawai ya yi furucin da ya ba kowa mamaki, ba tare da la’akari da cewa zato dai zunubi ne ba, ko da kuwa ya zama hakkun. Me ya hana Shugaba Jonathan gabatar da wata kwakkwarar hujjar da za ta tabbatar wa duniya cewa kungiyar Boko Haram da ya zarga ce ta aiwatar da waccan aika-aikar? Yana kuwa sane cewa kalamunsa abubuwan bibiya ne ga mutane masu kaifin hankali a nan cikin gida da kuma kasashen ketare? Ai bai kamata ya yi zarbabiya haka  ba, musamman ma ganin ba a yi cikakken bincike ba, kuma furucinsa na iya sauya rawar da jami’an tsaro za su taka dangane da  sakamakon da za su fitar.
To, a game da haka sai ga shi nan jam’iyyar PDP  ta nuna wa jam’iyyar APC yatsan zargi ita ma, sa’ilin da Babban Sakatarenta na  Yaba Labarai, Cif Olisa Metuh ya ce shugabannin jam’iyyar APC ne ke da alhakin kai harin, domin wai sun lashi takobin taka wa gwamnatin Shugaba Jonathan birki. Wannan dai ba sabon abu ba ne ga jam’iyyar PDP, domin kuwa ta saba bata mutuncin jam’iyyar da kuma shafa wa shugabanninta bakin fentin addini. Baicin haka nan kuma ba shi da hujjar furta haka, kuma ’yan APC din na iya kai shi kotu. Ko a ’yan kwanakin baya sai da ta yi kazafin cewa wai jam’iyyar APC na shirin tsayar da ’yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa Musulmi zalla don dai ta bata su a idanun mabiya addinin Kirista. Kuma ko a lokutan baya, jam’iyyar ta sha shafa wa Janar Muhamadu Buhari bakin fentin addini, ba don komai ba, sai don addininsa da bangaren da ya fito.
Yanzu ’yan Najeriya sun tabbatar da cewa lusarancin shugabannin kasar nan ne ya hana a shawo kan matsalolin tsaro, aka kuma kasa gano masu assasa haka duk da cewa ba daga sama suke fadowa ba, suna nan a cikin jama’a. To tun da jam’iyyar PDP tana ta shan zargi game da haka, babu kuma abin da ta iya, shi ya sa take zargin abokiyar adawarta, domin an ce idan duka ya yi yawa na kai ake karewa.