Zauna-gari-banza sun kona motar tumatir a Enugu
Sun kona motar kayan abinci da sunan tabbatar da umarnin IPOB na zama a gida.
Zauna-gari-banza sun kona wata motar tumatir da sauran kayan abinci a Jihar Enugu kan saba umarnin zaman gida na haramtacciyar kungiyar IPOB.
A ranar Litinin da safe ne zauna-gari-banza suka tare motar da ke dauke da tumatur da sauran kayan gwari a hanyarta ta shiga garin Enugu, suka cinna mata wuta da sunan dabbaka umarnin na IPOB.
- An gano maboyar gidan rediyon kungiyar IPOB
- Dakarun Nijar sun ceci sojojin Najeriya daga harin ’yan bindiga
A baya-bayan nan kugiyar ta yawaita neman tilasta wa mutane zaman gida a ranakun Litinin a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, lamarin da ke kara kazancewa.
An tare motar kayan abincin ne a mahadar Edem Ibeagwa da ke Nike a Karama Hukumar Enugu ta Gabas, bayan fitowar motar daga yankin Ugwogo da ke hanyar Opi zuwa Enugu.
Shaidun gani da ido sun sanar da hukumar kashe gobara game da danyen aikin na zauna-gari-banzan, inda daga bisani jami’anta kashe gobara suka kashe wutar.
“Abin da mutanenmu suka yi bai dace ba, saboda an tafka babbar asara, wanda bai kamata ba; Da mutanenmu sun yi tunani mai zurfi da ba su aikata hakan ba,” inji wasu shaidun gani da ido.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Enugu ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce kawo yanzu babu wanda aka kama.
A baya-bayan nan dai kungiyar ta IPOB, mai neman ballewa daga Najeriya ta kafa kasar Biafra, ta ce za ta janye matakin nata na sanya mutane zama a gida a yankin Kudu maso Gabas, a yayin da zauna-gari-banza ke amfani da damar sun cin zarafin mutane da tsula tsiyarsu.
A makon da ya gabta, mazauna garin Enugu sun yi watsi da umarnin IPOB din na ranar Litinin-Litinin, sai dai daga baya an yi ta jin karar harbe-harbe a garin, wanda hakan ya tilasta wa mutane tserewa zuwa gidajensu domin tsira da rayukansu.