Zaunar da makiyaya wuri daya: Rikicin manoma da makiyaya ya kawo karshe -Miyetti Allah
A makon da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da wani tsari da zai sanya makiyaya su daina yawo su rika zama wuri daya, Aminiya ta tuntubi na Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na kasa Alhaji Bello Badejo domin jin ko kungiyarsu ta yi maraba da wannan tsarin ko kuma tana […]

A makon da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da wani tsari da zai sanya makiyaya su daina yawo su rika zama wuri daya, Aminiya ta tuntubi na Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na kasa Alhaji Bello Badejo domin jin ko kungiyarsu ta yi maraba da wannan tsarin ko kuma tana ganin akwai matsala? Inda ya yi bayani kamar haka:
Aminiya: Da farko za mu so ka gabatar da kanka?
Bello Bodejo: Sunana Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal hore ta kasa.
Aminiya: A kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta sanar da aniyar fara hana yawo da dabbobi wajen kiwo tare da shirin samar wa makiyaya wuraren kiwo, mene ne matsayinku a kai?
Bello Bodejo: Wannan abu ne wanda muka jima muna neman a yi, kusan a ko’ina a duniya a halin yanzu Najeriya ce kadai makiyayanta ke yawon kiwo, yawanci wurare ake kebe musu su gudanar da al’amuransu ba tare da fuskantar fitintinu ba, kuma ko a nan din ma ai dama akwai wuraren wadanda aka yi su tun lokacin Turawan mulkin mallaka, amma saboda watsi da aka yi da su a baya da kuma karuwar jama’a, kusan an rasa wuraren a ko’ina a yanzu. To muna maraba da wannan shiri wanda muka jima muna kiraye-kirayen a yi. Ko ba komai zai taimaka wajen karuwar halartar makarantu a bangaren ’ya’yan Fulani makiyaya tare da magance rigingimu da suke fuskanta tsakaninsu da manoma.
Aminiya: Ko gwamnati ta tuntube ku a yayin yanke wannan shawara, idan ko ba ta tuntube ku mene ne shawararku a kai?
Bello Bodejo: A gaskiya gwamnati ba ta tuntube mu a kai ba, sai dai mun san akwai Fulani a cikin wannan kwamiti da ya bada wannan shawarwari kuma gwamnati ta amince, shugaban kwamitin wanda tsohon gwamnan Jihar Adamawa ne Murtala Nyako ai Bafulatani ne, kafin mataimakinsa a kwamitin, watau Gwamnan Jihar Binuwai ya amshi ragamar jagorancin kwamitin a yanzu. Haka ma sauran gwamnoni wadanda mambobi ne a ciki. Sai dai da sun tuntube mu da mun kara sanar da su wadansu abubuwan da muka sani kuma muke fuskanta, kasancewar mu ne makiyayan, muna zaune a jeji, kuma muna fuskantar al’amuran a kullum.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne kuke ganin ya kamata a samar a irin wadannan wuraren don ganin an samu amincewar makiya?
Bello Bodejo: Abun gwamnati dai sai su, ai a yanzu haka nan akwai Fulanin da suka share sama da shekara saba’in suna zaune a waje guda, su suka sari wurare suka fara zama a wajen, amma da wani abu ya faru sai ka ji an ce da su baki, to ire-iren wadannan matsaloli ya kamata gwamnati ta bai wa muhimmanci, a tabbatar musu da zama a wuraren, ba wai a rika yi musu kallon baki ba. A kuma samar da makarantu da cibiyoyin lafiya da madatsun ruwa, kuma a yanzu haka akwai wurarenmu da dama masu madatsun ruwa da aka samar tun a lokacin Turawan mulkin mallaka wadanda suka kirkiro da wuraren kiwo na baya, amma yanzu manoma suka mamaye su. To yana da kyau a sake dawo da wadansu daga cikin wuraren nan sannan a kirkiro wadansu sabbi.
Aminiya: Kamar wadanne jihohi ne kake ganin ake da makiyaya da ya kamata a yi wadannan wurare?
Bello Bodejo: Ai kusan babu wata jiha, ko ma in ce da kai karamar hukuma, da babu Fulani makiyaya a ciki, sai dai a ce wadanne jihohi ne suka fi yawa, sannan ina ne ake da wuraren kiwon da za a yi masu kari, sannan ina ne babu su kwata-kwata. Ka ga kamar Jihohi irin su Taraba da Adamawa, da dai sauransu, akwai irin wadannan wurare har yanzu, kamar wani da na sani da ke Sunkani wajen yankin Gembu a Jihar Taraba, ko shi kadai aka bude aka inganta zai dauki makiyaya masu yawa. Kuma na ji a cikin shawarwari da suka bayar har da na bukatar samar da Naira Biliyan 100 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) don samar da ayyukan da za a yi a wadannan wurare. To shawararmu a nan ita ce, su jawo Fulani da sauran masu ruwa da tsaki a wannan harka don ganin an yi abun yadda ya dace, ai dama an ce da dan gari akan ci gari.
Aminiya: Jihar Binuwai na daya daga cikin wuraren da makiyaya ke da tarin yawa, kwatsam bayan tashe-tashen hankulan da suka addabi jihar a kwanakin baya, sai Fulani suka yi ta barin wajen, wane hali ake ciki a can a yanzu?
Bello Bodejo: Wannan haka ne, har ma da jihohi irinsu Kaduna da Katsina da Filato da kuma Zamfara, sai dai a sakamakon wani kwamiti da tsohon Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya Alhaji M.D Abubakar ya kafa, wanda ni mamba ne a kwamitin, an samu nasarori sosai, ba ni mancewa mun samu kwana dai-dai har biyar a Binuwai lokacin da rangadi ya kai mu wajen, a lokacin kusan babu wadansu Fulani da suka rage a wajen, amma ba mu bar wajen ba sai da kwamitinmu ya tabbatar da yawancin Fulanin da suka yi hijira daga wajen sun koma. An gayyato shugabannin Miyetti Allah da na kabilar Tibi an rattaba hannu, ni ma a matsayina na jagoransu na kasa na sa hannu, haka muka yi a Jihar Nasarawa da sauran jihohi da irin wannan al’amari ya shafa. Kuma Alhamdu lilLahi tun daga wancan lokaci ba mu sake jin wata fitina ta sake tashi a Jihar Binuwai ba.
Aminiya: Fulani sun samu kansu a cikin halin tsaka mai wuya a dan tsakanin nan, kusan fiye da dukkan wani lokaci, kwatsam sai ga bayani a makon da ya gabata kungiyarku na bukatar a sake zabar wannnan gwamnati mai mulki, me ke faruwa ne ?
Bello Bodejo: E…… sauyawar al’amura ne, da Fulani ake siyasa, da su ake wannan gwamnatin, amma sai suka zamo tamkar ’yan bora, ba a damu da al’amuransu ba. Idan ka duba shugaban jamiyyar gwamnati mai ci Ahmadu Mu’azu Bafulatani ne, Ministan Abuja Bala Muhammad Bafulatani ne, mai bai wa shugaban kasa shawara a harkar siyasa Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali Bafulatani ne, Sakatare na musamman na shugaban kasa Ambasada Hassan Tukur Bafulatani ne, a bangaren gwamnonin Arewa na yanzu kusan daukacinsu ba sai na lissafa maka su ba, idan aka bi tsatsonsu Fulani ne kuma Borori na daji suka dawo birni. Ashe mu ci gaba da zama cikin wadannan hali alhali mu ke rike da gwamnati, ba don komai ba sai don kawai ana ganin a bangarenmu na makiyaya ba ma tare da gwamnati, ba dabara ba ce, to idan dai zan takaice maka, larura ce ta sa mu yin hakan, kuma mun amince za mu yi wannan gwamnati dari bisa dari.
Aminiya: Ana ganin Fulani makiyaya na baya-baya wajen kada kuri’a a yayin zabe, wane shiri kuke yi wajen wayar musu da kai a kan wannan?
Bello Bodejo: Wannan na daga cikin abubuwan da muka sa a gaba, akwai wani tsari da muka fitar na yi musu bayani a kan al’amarin siyasa da sauran al’amura, da muka bai wa suna ‘’Ruga zuwa ruga’’, inda za a yi wa Fulani bayanin muhimmancin mallakar kuri’a da kuma amfani da shi wajen shiga harkar kasa, kuma insha Allahu za a ga sauyi a game da halartar zabe a bangaren makiyaya a wannan zabe na 2015 da ke tafe.