Zaven Kogi: Hukumar INEC ta raba gardama

Hukumar Zave ta Qasa (INEC) ta bai wa jam’iyyar APC damar gabatar da sabon xan takarar gwamna a ci gaba da zaven Jihar Kogi, sakamakon mutuwar xan takarar jam’iyyar Prince Abubakar Audu a ranar Lahadin da ta gaata.Hakazalika, Hukumar ta sanya ranar 5 ga watan gobe ranar don kammala zaven jihar a mazavu 91 waxanda […]

Zaven Kogi: Hukumar INEC ta raba gardama

Hukumar Zave ta Qasa (INEC) ta bai wa jam’iyyar APC damar gabatar da sabon xan takarar gwamna a ci gaba da zaven Jihar Kogi, sakamakon mutuwar xan takarar jam’iyyar Prince Abubakar Audu a ranar Lahadin da ta gaata.
Hakazalika, Hukumar ta sanya ranar 5 ga watan gobe ranar don kammala zaven jihar a mazavu 91 waxanda aka soke zaven da aka gudanar a qarshen makon jiya.
A ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar jihar suka kaxa quri’unsu don zavar gwamna. Kuma bayan kammala tattara quri’un ne sai hukumar zave ta ce sakamakonn zaven bai kammalu ba. Saboda bambancin quri’un da ke tsakanin xan takarar jam’iyyar APC da kuma na PDP bai xara yawan quri’un da aka soke a mazavu 91 ba. Kodayake, marigayi Abubakar Audu shi ne yake kan gaba yayin da Gwamna Idris Wada yake biye da shi. Kuma bambancin quri’un da ke tsakaninsu su ne 41,353 yayin da yawan quri’un da aka soke ya kai guda 49,953. Hukumar tana ganin idan aka sake zavuka a mazavun da aka soke, to wata qila sakamakon zaven yana iya sauya alqibla.
Daga nan ne kuma gardama ta varke tsakanin lauyoyi, inda wasu suke kira da a sake sabon zave a gaba xayan jihar saboda rasuwar Abubakar Audu gabanin sanar da sakamakon qarshe na zaven. Har ila yau, akwai masu ra’ayin a bai wa mai mara masa baya wato Mista James Faleke damar maye gurbin kujerar mamacin. Hakazalika, akwai wasu masu ra’ayin cewa a bai wa jam’iyyar damar gudanar da sabon zaven fidda gwani don gabatar da wani sabon xan takara kamar yadda  hukumar INEC ta buqaci jam’iyyar APC ta yi a ranar Talatar da ta gabata.  
Kamar yadda sashe na 36 sakin layi na farko na dokar zave ya bayyana idan wani xan takara ya mutu gabanin ranar zave, za a bai wa jam’iyyarsa damar maye gurbinsa da wani xan takara sabo. Wannan ya sa wasu suke da tunanin cewa abin da ya fi dace wa kan batun zaven shi ne a sake sabo gaba xaya.
Hakazalika, doka ta yi tanadin cewa idan zavavven gwamna ya rasu gabanin rantsar da shi zavavven mataimakinsa ya maye gurbinsa. Hakan ya sa galibin masana suke bayyana cewa abu ne da ba a tava cin karo da irin sa ba, inda xan takara ya rasu kafin kammala zave.
Kodayake, jam’iyyar APC ta ce za ta gudanar da sabon zaven fidda gwani kamar yadda hukumar INEC ta buqata.