Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 36 a Edo

“Muna sa ido sosai kan lamarin, kuma tawagar sa ido tamu tana aiki don gano ɓullar cutar da tuntuɓar juna.”

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 36 a Edo

Gwamnatin Edo ta sanar da cewa zazzaɓin Lassa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 36 a jihar tun daga farkon shekarar 2024 kawo yanzu.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta bayar da rahoton cewa ana zargin wasu mutum takwas sun kamu da cutar kwalara ta amai da gudawa.

Darakta a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Ojeifo Stephenson, wanda ya bayyana hakan, ya ce an gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ne a ranar Alhamis a cikin majinyata 16 da ke kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH).

Dokta Stephenson, ya ce an fitar da alƙaluman ne bayan gudanar da gwaje-gwajen gaggawa (RDT) ga dukkan majinyata 16.

Ya bayyana cewa, “Duk da cewa gwaje-gwajen babu tabbaci a kai, an kuma aika da samfurin marasa lafiyar zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ƙasa da ke Abuja, don tabbatarwa.”

Saboda haka ya jaddada cewa, ba za a bayyana samun ɓullar cutar kwalara ba har sai an tabbatar da sakamakon binciken daga ɗakin bincike na ƙasa.

A halin da ake ciki, ya ce jihar na haɗa kai da wata tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) domin shawo kan lamarin.

Dokta Stephen ya buƙaci mazauna yankin da kada su firgita, yana mai ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar tare da goyon bayan ma’aikatan hukumar lafiya ta duniya WHO na gudanar da bincike yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa, “Muna sa ido sosai kan lamarin, kuma tawagar sa ido tamu tana aiki don gano ɓullar cutar da tuntuɓar juna.”

Ya kuma shawarci al’umma da su kula da tsaftace muhallinsu da kuma kai rahoton duk wani wanda ake zargi ya kamu ga cibiyar lafiya mafi kusa.