Zazzabin Lassa da Kwalara sun sako ’yan Najeriya a gaba

NCDC ta ce a bana kadai akwai jihohi 10 da kowaccensu ta samu bullar cutar.

Zazzabin Lassa da Kwalara sun sako ’yan Najeriya a gaba

Cutar Kwalara ta ci rayukan mutum 3,604 cikin jihohi 33 da kuma babbar birnin kasar wato Abuja kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar.

Daga cikin jihohin da lamarin ya shafa sun akwai Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Binuwai, Borno, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Filato, Sakkwato, Taraba, Yobe, Ribas da Zamfara.

A alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Litinin, ta ce an samu mutum 111,062 da suka kamu da cutar a bara, inda galibi yara maza da mata ’yan tsakanin shekarun haihuwa 5 zuwa 14 suka fi kamu da ita.

Hukumar NCDC a jiyan ta kuma ce an samu mutum 222 sabbin kamuwa da cutar zazzabin Lassa kuma ciki biyu sun riga mu gidan gaskiya tun a makon farko na shekarar 2022 da muka yi maraba da ita.

A rahoton, NCDC ta ce a bana kadai akwai jihohi 10 da kowaccensu ta samu bullar cutar.

Jami’ar da ke kula da barkewar cututtuka masu yaduwa a Jihar Filato, Matina Alex Nuwan ta ce sun tabbatar da gwajin mutum guda da ya harbu da cutar yayin da mutum tara ke jiran sakamakon gwajin cutar.

A bayan nan dai zazzabin Lassa ya yi ajalin mutane da dama a yankin Oke-Ogun da ke Jihar Oyo, wanda a kan haka ne Kwamishinan Lafiyar Jihar, Bode Ladipo a Litinin din da ta gabata ya sanar cewa gwamnati ta kafa kwamitin kwararru domin dakile yaduwar cutar a duk kananan hukumomin da ke jihar.

Hukumar ta NCDC ta ce mutum dari da biyu ne suka mutu da cutar ta Lassa a Najeriya a bara.