Zazzabin Lassa: Muna sa ran matakan da muka dauka za su kwantar wa Saudiyya hankali – Hukumar Hajji

Aminiya: Bayanan da ke yawo a yanzu su ne kasar Saudiyya tana yunkurin hana ’yan Najeriya zuwa aikin Hajji a bana sakamakon bayyanar cutar zazzabin Lassa feber a wasu yankunan kasar nan, mai za ka ce? Abdullahi Modibbo Saleh: To alhamdulillahi, wannan bayani ba gaskiya ba ne. kasar Saudiyya ba ta yin yunkurin hana maniyyatan […]

Zazzabin Lassa: Muna sa ran matakan da muka dauka za su kwantar wa Saudiyya hankali – Hukumar Hajji

Aminiya: Bayanan da ke yawo a yanzu su ne kasar Saudiyya tana yunkurin hana ’yan Najeriya zuwa aikin Hajji a bana sakamakon bayyanar cutar zazzabin Lassa feber a wasu yankunan kasar nan, mai za ka ce?

Abdullahi Modibbo Saleh: To alhamdulillahi, wannan bayani ba gaskiya ba ne. kasar Saudiyya ba ta yin yunkurin hana maniyyatan Najeriya zuwa aikin Hajji. Sai dai abin da ya faru shi ne, abu ne da kasar ta saba yi a kullum daga cikin matakan da take dauka wanda ake sa rai al’ummar duniya gaba daya musamman ma mahajjata an kare su daga duk wani abu da zai cutar da lafiyarsu. Kuma kasar Saudiyya tana da hakkin al’umma da yawa na kasashen da suke zuwa aikin nan da kuma al’ummarta. To sun samu labari kamar yadda kowace kasa take iya samun labari a kan abubuwan da suke faruwa a wasu kasashe. A irin haka ne ta samu labarin cewa an samu matsalar barkewar cutar zazzabin Lassa a wasu yankunan kasar nan, kuma a dalilin haka suka yanke shawarar daukar wasu matakai don ganin sun kare al’umma. A namu bangaren mun dauki matakai da dama bayan samun wannan labari ko a yau din nan Talata Hukumar Hajji ta kasa ta gana da Ministan Lafiya inda ya tabbatar da cewa lallai akawai matsalar bayyanar cutar a wasu yankunan kasar nan kuma ana dukan kokarin ganin an shawo kan matsalar. Bayanin da muka samu shi ne matsalar aukuwarta ta bayyana ne a jihohi 3 da suka hada da wani gari a Jihar Ondo da wani garin a Jihar Edo sai kuma wani gari a Jihar Ebonyi. Haka a tsakanin shekaranjiya da jiya har zuwa yau din nan (shekaranjiya Laraba), Hukumar Hajji ta kasa ta shirya taron tattaunawa a tsakaninta da kamfanonin jigilar mahajjata da likitocinsu da kuma Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya inda aka tsara wasu matakai da ake son a aiwatar da su da suka hada da gudanar da bincike a kan maniyyata a kan wannan lamari da ma duk wata cuta kafin a fara tafiya zuwa aikin Umarah. Kuma insha Allahu wannan mataki zai ci gaba har zuwa lokacin aikin Hajji da zai hada har da kan kayan maniyyata kamar yadda dama aka saba yi. Insha Allahu muna sa rai wadannan matakan da muka dauka za su kwantar wa kasar Saudiyya da hankalinta kamar yadda mu hankalinmu ya kwanta tuntuni.

To wannan kamar wane sharadi ta gitta muku da take bukatar ku cika kafin a ba ku damar kai maniyyatan?

A’a, ba wani sharadi da suka gitta mana. Sai dai dama sharrudan kiwon lafiyai ai sanannu ne wadanda kuma Ma’aikatar Lafiya ta kasar nan ke aiki hannu-da-hannu a kansu da Hukumar Lafiya ta Duniya da sauran kasashe ciki har da kasar Saudiyya da ake aiwatar da su. Ba wai a kan aikin Hajji kadai ba, wannan lamari ne na yau da kullum da ake gudanar da shi a harkar zirga-zirga ta duniya da sauran al’amura na gida wadanda ba sai aikin Hajji kadai ba.

Ko akwai wata sanarwa da ta auku a tsakaninku da kasar Saudiyya a kan wannan lamari?

Bayanin ya fito ne ta Ma’aikatar Lafiya ta kasa wadda ta mika shi ga Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Sama, cewa sun samu labarin bayyanar cutar zazzabin Lassa a Najeriya saboda haka suka ba su umarnin su dauki matakan da suka kamata na kare al’umma. To su kuma Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama sai suka sanar da sauran takwarorinsu na duniya baki daya da lamarin inda daga cikin cututtukan da suka sanar da su har da wannan matsalar da suka ji rahotun bayyanarta a kasar nan. 

To bayan kun samu wannan sanarwa wadanne matakai kuka dauka a bangarenku don ganin kun tsallake wannan siradi?

Abu na farko da muka dauka shi ne ganawa a tsakaninmu da jami’an Ma’aikatar Lafiya ta kasa wadanda dama muna yin aiki da su kafada-da-kafada a karkashin jagorancin babban wakilinsu da ke hulda da mu, shi kuma ya kira sauran takwarorinsa da ke wakiltar ma’aikatar a wasu hukumomi kamar NCAA da FAAN aka tattara rahoto aka mika wa Gwamnatin Tarayya. Kuma a dalilin haka Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha ya kira taro na dukan masu ruwa-da-tsaki a lamarin a yau din nan (shekaranjiya Laraba) taron da ya hada da ma’aikatu uku na Harkokin Waje da na Kiwon Lafiya da ta hado daukacin kwamishinonin kiwon lafiya na jihohi da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da kuma hukumomin da ke karkashin ma’aikatar, sai kuma Hukumar Hajji ta kasa, aka gana a dakin taro na Sakataren Gwamnatin Tarayya a kan lamarin tare da nuna wa kasar Saudiyya cewa yadda take jin rahoton lamarin nan, bai kai ga haka ba, wasu yankunan kasar nan ne kalilan aka samu rahoton aukuwarsa kuma ana daukar kwararan matakan magance su.

Ana daf da fara tafiya aikin Umarah, shin ko wannan rahoto yana iya shafarsa?

Komai yana nan yana tafiya kamar yadda aka tsara, kuma insha Allahu wannan al’amari ba zai shafi shirin Umara ba. Ko a yau din nan (shekaranjiya Laraba) mun gana da kamfanonin masu jigilar maniyyata Umarar nan an yi zama da su tare da sauran masu ruwa-da-tsaki a lamarin inda aka tattauna a kan al’amura da kuma yadda za a kyautata su.