Zazzabin Lassa ya kashe mutum biyu a Filato
Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Cletus Shurkuk, ya sanar cewa mutum na uku da ya kamu da cutar yana samun kulawa a asibiti.
Mutum biyu sun rasu sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a Jihar Filato.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Cletus Shurkuk, ya sanar cewa mutum na uku da ya kamu da cutar yana samun kulawa a asibiti.
Ya bayyana cewa mamatan sun kamu da cutar ne a Karamar Hukumar Kanam, na ukun da ke raye kuma a Karamar Hukumar Shendam.
Daya daga cikin majinyatan ya rasu ne a Shendam na biyun kuma a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
- Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamanatin jihar tana aiki tare da Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) domin dakile yaduwar cutar.
Ya ce tun da suka samu rahoton bullar cutar suka tura jami’ansu zuwa yankunan domin yin gwaji ga wadanda suka yi mu’amala da marasa lafiyan da kuma wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariyar cutar.
Ya shawarci al’ummar jihar da su kasance masu kula da tsaftar muhalli domin dakile yaduwar cutar.