Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 10 a Ebonyi

Daga cikin wadanda suka mutu har da mace mai juna biyu.

Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 10 a Ebonyi

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Ebonyi, ta tabbatar da mutuwar mutum 10 sakamakon kamuwa da zazzabin ciwon Lassa a jihar, daga ranar 4 ga watan Janairu zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2024.

Jami’in kula da cututtuka na ma’aikatar, Mista Sampson Orogwu, ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abakaliki.

Orogwu, ya bayyana cewa mutum 25 ne suka kamu da cutar, ciki har da ma’aikatan lafiya biyu.

Ya kara da cewa “16 daga cikin 25 da suka kamu da cutar maza ne, yayin da tara kuma mata ne.

“Wadanda suka mutu sun hada da mace mai ciki da yara biyu da kuma maza bakwai.

“Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da: Onicha, Ikwo, Ezza ta Arewa, Ebonyi, Izzi, Ohaukwu da Abakaliki tare da yankin Nkaliki a Abakaliki wanda yake a yawan masu dauke da cutar.”

Don haka, ma’aikatar ta bukaci mazauna yankin da su kai rahoton duk wanda ya kamu da cutar ga ma’aikatar.

Zazzabin Lassa wata cuta ce da wani nau’in ɓera ke yada ta, kuma cutar tana yaduwa cikin sauri.

Yawanci mutane kan kamu da cutar ta Lassa ta hanyar kamuwa da abinci ko kayan aikin gida da suka gurbata da fitsarin beraye.

Cutar dai ta zama ruwan dare musamman a yankin a Afirka ta Yamma.

Daga cikin alamun cutar akwai zazzabi, amai, ciwon kai mai tsanani, ciwon jiki da sauransu.