Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 8 a Ondo
Mutum 106 aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin Jihar Ondo.
Gwamnatin Jihar Ondo ta ce mutum takwas sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyar Zazzabin Lassa.
Wannan dai na daga cikin mutum 106 da aka tabbatar sun kamu cutar a bana.
- A karo na 5, Akwa Ibom ta lashe kambun Jiha mafi tsafta a Najeriya
- INEC ta sake kara wa’adin karbar katin zabe
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan sha’anin kiwon lafiya, Fafesa Francis Faduyile ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Lahadi a Akure, babban birnin jihar.
“Daga 1 zuwa 23 ga Janairu, mun samu mutum 268 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da kuma aka tabbatar 106 sun kamu, sannan ta kashe mutum takwas,” in ji Faduyile.
Ya ce wadanda aka tabbatar da sun harbu da zazzabin sun fito ne daga kananan hukumomi shida a jihar da suka hada Owo da Akure ta Arewa da Akure ta Kudu da Ose da Akoko ta Kudu maso Yamma, sai kuma Idanre.
Ya kara da cewa, zazzabin ya fi ta’azzara a lokacin zafi da kuma wani bangare na damina.
“Barin kona daji da kiyaye abinci daga beraye a gida na daga cikin hanyayoin yaki da yaduwar Zazzabin Lassa,” in ji jami’in.
(NAN)