Zazzabin Lassa ya yi kisa a Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar wata mata ’yar shekara 28 a sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa.Matar mai suna Eze, wadda ’yar asalin Jihar Ebonyi ce, ta kamu da cutar ce bayan da ta yi bulaguro zuwa jiharsu, inda ta halarci bikin binne wani mamaci dan uwanta; wanda ba a san musababbin mutuwarsa […]

Zazzabin Lassa ya yi kisa a Ogun
Zazzabin Lassa ya yi kisa a Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar wata mata ’yar shekara 28 a sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
Matar mai suna Eze, wadda ’yar asalin Jihar Ebonyi ce, ta kamu da cutar ce bayan da ta yi bulaguro zuwa jiharsu, inda ta halarci bikin binne wani mamaci dan uwanta; wanda ba a san musababbin mutuwarsa ba. Bayan da ta dawo Ogun ne ta kamu da zazzabi, wanda daga bisani aka tabbatar da cewa cutar zazzabin lassa ce.
A halin yanzu hukumar lafiya a jihar ta sanya idanu a kan mutum 121, wadanda suka yi mu’amala da matar, wadanda yawancinsu ma’aikatan asibiti mai zaman kansa ne, inda aka fara kwantar da ita. A cewar Kwamishinan Lafiya na Jihar Ogun, Dokta Babatunde Ipeye, matar ta rasa ranta ne a ranar Asabar din da ta gabata kuma za a binne ta bisa ka’idojin Hukumar Lafiya ta Duniya, bayan da iyalanta suka ba gwamnatin jihar izinin yin hakan.
Hakazalika, wata mata mai juna biyu ’yar shekaru 28 ta kamu da cutar ta zazzabin Lassa a jihar a karo na biyu, wacce ita ma ta yi bulaguro ne daga Jihar Kogi; wacce a yanzu haka ake kula da lafiyarta kuma tana kan murmurewa. Ana kuma sanya idanu a kan mutun 60 da ta yi mu’amala da su, wanda ya ba da jimillar mutum 181 da a yanzu hukumar lafiya ta jihar ke sanya wa idanu.
A wata sabuwa kuma, wani malami a Jami’ar Redeemers ta Ede a Jihar Osun, Farfesa Christian Happi ya bayyana cewa jinsin kabilun Yarabawa na da juriyar rashin kamuwa da cutar Lassa. Ya ce a yanzu suna kan yin bincike, wanda ya kai su ga gano hakan, ya shaida cewa dukkanin rahotannin annobar cutar Lassar da aka samu a ’yankunan Yarabawa daga wasu yankunan aka shigo da su. Ya kara da cewa, cutar zazzabin Lassa ta samo asali ne a Najeriya fiye da shekaru 1,060 kuma kabilun Yarabawa ka iya jure wa kwayar cutar fiye da duk wata kabila a Najeriya.