Zelensky ya saduda: Ukraine ta hakura da shiga kungiyar NATO
Zelensky ya ba da kai bori ya hau kan bukatar Rasha cewa kada kasarsa ta shiga kungiyar NATO
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce kasarsa ta hakura da batun zama mamba a Kungiyar Tsaro ta NATO, wanda shi na babban abin da ya sa Rasha ta mamaye kasar tasa.
Bayan ya ba da kai bori ya hau game da bukatar Rasha ta janye yunkurin kasars na shiga kungiyar NATO, Zelensky ya kara da cewa a shirye Ukraine take ta sauya matsayin da ta dauka kan wasu yankunanta biyu na kasar da Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya aminta da su a matsayin masu cin gashin kansu, kafin ya far wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
- Wainar da ake toyawa a yakin Rasha da Ukraine
- Rikicin Ukraine: Farashin gangar danyen mai zai iya kai wa $300 – Rasha
“Na dade da hucewa game da wannan batu tun bayan da muka fahinci cewa…NATO ba ta shirya karbar Ukraine a cikinta ba.
“Kungiyar kawancen tana tsoron abubuwa masu sarkakiya ko yin fito-na-fito da Rasha” inji Zelensky a zantawarsa da kafar yada labarai ta ABC a ranar Litinin.
Ya kara da cewa kasarsa ba ya son ya kasance shugaban “kasar da sai ta durkusa a kan gwiyawunta saboda tana bukatar wani abu”.
Rasha dai ba ta son makwabciyarta Ukraine ta shiga kawancen na NATO da aka kafa domin fara yakin cacar baka domin kare kasashen Yammacin Turai daga tsohuwar Tarayyar Soviet.
A shekarun baya-bayan nan, NATO ta kara yawan mambobinta daga Gabashin Turai, daga cikin kasashen da suka yakice daga Tarayyar Turai, matakin da ya fusata Rasha.
Rasha dai na ganin karin yawan mambobin NATO a kusa da ita matsayin barazanar tsaro a gare ta.
Jim kadan kafin ya far wa Ukraine da yaki, Putin ya aminta da yankunan ’yan aware, Lugansk da Donetsk, da suke yaki da Ukraine tun 2014 a matsayin kasashe masu ’yanci.
Yana kuma so Ukraine ta dauki yankunan biyu a matsayin kasashe masu cikakken ’yancin cin gashin kansu.