Zelensky ya roki Birtaniya ta horar da sojojin Ukraine don yakar Rasha

Birtaniya ta yi Ukraine alkawarin soja 10,000

Zelensky ya roki Birtaniya ta horar da sojojin Ukraine don yakar Rasha

Birtaniya ta yi wa Ukaine alkawarin sojoji 10,000 bayan Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya nemi ita da kawayenta su taimaka masa da sojoji da za su ba wa sojojin kasarsa horo na musamman a ci gaba da yakin da suke yi da Rasha.

A ziyararsa ga Majalisar Dokokin Birtaniya bayan ganawarsa da Sarki Charles III, Zelensky ya ce akwai bukatar Birtaniya ta taimaka wa Ukraine wajen yakar Rasha.

Yayin da ake ci gaba da kazamin fada a Gabashin Ukraine, Zelensky ya ce lokaci ya yi da kasashen Turai za su taimaka wa Ukraine da jiragen yaki da makamai masu linzami don durkusar da Rasha.

Bayan ganawarsa da ’yan Majalisar Birtaniya, an yi wa Zelensky alkawarin sojoji sama da dubu 10, da kuma matuka jiragen yakin da za su horas da dakarun kasarsa.

Fira Minista Birtaniya, Rishi Sunak ya yi, ya ce Birtaniya za ta taimaka wa Ukraine da sojoji da kayan yaki, amma hakan zai dauki lokaci kafin a yi.

A cewarsa a yanzu za a tabbatar da fara horar da matuka jiragen yakin Ukraine kan tuka jiragen yaki na zamani da Kungiyar Tsaro ta NATO ta samar wa kasar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos