Zelenskyy ya wajabta kwashe mutane daga Donetsk bayan Ukraine ta kashe sojojin Rasha
Zelenskyy ya wajabta kwashe mutane a Donetsk bayan dakarunsa sun hallaka sojojin Rasha
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ba da umarnin a kwashe matanen kasar ala tilas kuma cikin gaggawa daga Lardin Gabashin Donetsk.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Ukraine suka hallaka sojojin Rasha kimanin 100 a wani kazamin fada a yankin Kherson.
- Ya kamata a debi matasa miliyan 5 aikin dan sanda — Basaraken Iwo ga Buhari
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Ke Kallon Batun Tsige Buhari
A cikin wani sakon bidiyo, Zelenskyy ya shaida wa ’yan kasar cewa, “Gwamnati ta riga ta ba da umarni a kwashe mutane daga yankin Donetsk ala tilas.
“Saboda haka wajibi ne kowa ya bi wannan umarnin, saboda a wannan mataki, babu wani babban makamai da Rasha ke da shi fiye da ta’addanci.”
Ya ce dubban daruruwan mutane na ci gaba da zama a yankin Donbas inda ake ci gaba da gwabza kazamin fada.
Don haka bukaci ’yan kasar da cewa “Duk wanda zai iya ya yi magana da mutanen da har yanzu suke zaune a inda ake fada a Donbas.
“Ku fahimtar da su muhimmancin ficewarsu daga yankin, musamman tare da iyalansu, sannan idan kuna da hali, ku taimaka wa masu gudun hijira.”
Ya kuma yi wa mutanen kasar alkawarin tallafin kudade da na bukatun yau da kullum domin su taimaka wa masu neman mafakan daga wadancan yankunan da matsuguni.
A bangaren guda kuma, kafofin yada labaran Ukraine sun ruwaito Mataimakin Fira Ministan kasar, Iryna Vereshchuk, yana cewa ya kamata a gama kwashe mutane kafin a shiga lokacin kaka, saboda an riga an lalata hanyar samar da iskar gas a yankin.