Zidane ya zama sabon kocin Faransa

Zidane ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru huɗu da tawagar ƙwallon ƙafar Faransa.

Zidane ya zama sabon kocin Faransa

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Faransa (FFF), ta naɗa tsohon fitaccen ɗan wasan ƙasar, Zinedine Zidane, a matsayin sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafar maza ta ƙasar.

Naɗin, wanda aka sanar a ranar Talata, ya kawo ƙarshen dogon jiran da aka yi na ganin Zidane ya jagoranci Les Bleus, inda ya maye gurbin Didier Deschamps bayan kammala gasar Kofin Duniya ta 2026.

Rahotanni sun ce ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru huɗu.

Zidane, mai shekaru 54, na daga cikin fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da Faransa ta taɓa samu.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe Kofin Duniya na 1998 da kuma gasar cin kofin Turai ta 2000.

Bayan yin ritaya daga taka leda, Zidane, ya yi fice a aikin horarwa tare da ƙungiyar Real Madrid, inda ya lashe kofunan Gasar Zakarun Turai guda uku a jere, abin da ya sa ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu horar da ƙwallon ƙafa a duniya.

Ana sa ran sabon kocin zai fara shirya tawagar Faransa domin wasannin UEFA Nations League da kuma neman gina ƙungiyar da za ta fafata a gasar Euro 2028 da Kofin Duniya na 2030.