Zidane ya zama sabon kociyan Faransa
Zidane zai maye gurbin Didier Deschamps, wanda ya sauka bayan shafe shekara 14 yana jagorantar tawagar.
Zinedine Zidane
Rahotanni na cewa gwarzon ɗan wasan Faransa kuma tsohon kocin Real Madrid Zinadine Zidane ya rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar aikin horas da tawagar ƙwallon ƙafar Faransa, daga yanzu zuwa watan Yunin shekarar 2030.
Zidane zai maye gurbin Didier Deschamps, wanda ya sauka bayan shafe shekara 14 yana jagorantar tawagar.
- An kama wani mutum da ƙunshi 28 na tabar wiwi a Katsina
- Wani magidanci ya roƙi kotu ta tilasta wa ’yarsa fitar da mijin aure
Ɗan jaridar nan na Italiya, da ya yi fice wajen bayyanawa da tabbatar da labaran wasanni musamman kan sauyin sheƙar ’yan wasa, wato Fabrizio Romano ne ya bayyana ƙulla yarjejeniyar ta Zidane da ƙasarsa Faransa cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Wannan na nufin Zidane ne zai jagoranci wasannin da Faransa za ta haska cikinsu a gasar Lig ɗin ƙasashe ta UEFA a shekara mai zuwa, da kuma Gasar Kofin Nahiyyar Turai ta 2028, sai kuma Gasar Kofin Duniya ta 2030.
Zidane, mai shekaru 54 ya kasance babu aikin yi tun da ya rabu da Real Madrid a shekarar 2021, biyo bayan kome da ya yi wa ƙungiyar ta birnin Madrid.
A yayin zamansa a Madrid, Zidane ya jagoranci ƙungiyar zuwa ga lashe Kofin Zakarun Turai sau 3 a jere, a tsakanin shekarar 2016 da 2018, kana ya lashe kofunan La Liga 2, da sauran kofunan cikin gida da dama.
A matsayinsa na ɗan wasa, ya jagoranci Faransa ta lashe Kofin Duniya na 1998 da Euro 2000, kuma ya lashe Kofin Zakarun Turai da Real Madrid a 2002.