Zikirin bana ya hada dahiru Bauchi da Isiyaka Rabi’u a wuri daya
Shughaban kungiyar Matasan Sufaye ta Najeriya, Malam Sham’unu Sheikh Ali Musa Gabari, ya bayyana matukar farin cikin mabiya darikar Tijjaniyya, ganin yadda aka samu gagarumar nasarar gudanar da zikirin shekara-shekara a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, inda manya-manyan shehunnan darikar suka taru a karo na farko. Wannan taron zikiri da aka […]
Shughaban kungiyar Matasan Sufaye ta Najeriya, Malam Sham’unu Sheikh Ali Musa Gabari, ya bayyana matukar farin cikin mabiya darikar Tijjaniyya, ganin yadda aka samu gagarumar nasarar gudanar da zikirin shekara-shekara a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, inda manya-manyan shehunnan darikar suka taru a karo na farko.
Wannan taron zikiri da aka saba gudanarwa a fadar sarkin Kano a kowace shekara, a bana ya smau halartar manyan shehunnai da mabiyansu daga ko’ina a fadin Afirika ta Yamma, musamman daga Jamhuriuyar Nijar da Kamaru da Ghana.
A ganawar da ya yi da Aminiya, malamin ya bayyana matukatar farin cikinsa da na daukacin ’ya’yan kungiyarsa kan irin gagarumar nasarar da suka samu a zikirin na bana, al’amarin da ya danganta da haduwar kan shehunnai da mabiya a wuri guda.
Ya bayyana cewa, ba a taba samun lokacin da mafi yawan ’yan kungiyarsu ta Harakatu Shababul Sufiyya suka yi zama a irin wannan gagarumin taro da Sheikh dahiru Usman Bauchi da Khalifan Tijjaniya as-Sheikh Isyaka Rabi’u da manyan ’yan siyasa da ’yan kasuwa da daukacin wadanda a da aka dade ba a yi irin wannan zikiri tare da su ba, sai a wannan karo.
“Halifan Tijjaniyya Sheikh Isyaka Rabi’u ya zauna tare da Maulanmu Sheikh dahiru Usman Bauchi, har ma ’ya’yansa su Alhaji karami (Alhaji Rabi’u Isyaka Rabi’u) ya zo ya ce shehunmu ya yi masa addu’a. Wannan ba karamar nasara ba ce a taron zikirin bana, domin har Shugaban Majalisar Wakilai da kansa, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi godiya ga Allah da ya gan su a tare,” inji shi.
Ya ce: “Marigayi San Kano, Alhaji Ado Bayero ya zame wa darikar Tijjaniya tamkar wani jarmai, duk da yake ba abin mamaki ba ne ganin cewa mahaifinsa shi ya kawo mana Sheikh Ibrahim Nyass. To tun daga wannan lokacin gidan sarautar Kano yake hidima ga Tijjanawa. Yau kuma daga Halifa Sa Muhammadu Sunusi har Allah Ya kawo mu zamanin Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, wanda ya ci gaba da wannan hidima,” inji shi.
Shugaban matasan Sufayen ya karkare batutuwansa tare da mika godiyarsa ga Allah game da wannan gagarumar nasara da aka samu a zikirin bana. Ya kuma yi fatan alheri ga shugaban kwmaitin tsare-tsare, wato Shehi Shehi, dan marigayi Shehu Maihula.