Zimbabwe: Soja sun kori yaro daga makaranta kan alakar babansa da Jam’iyyar MDC-T

Sojoji sun kori wani yaro dan shekara biyar daga makaranta a kasar Zimbabwe saboda mahaifinsa na goyon bayan jam’iyyar adawa ta MDC-T.Yaron mai suna, Enos Choga, yana makarantar share fagen shiga firamare ce a barikin 1 Commando Barracks wadda doka ta ce wajibi ne ta dauki dukkan yara ciki har na fararen hula.Mahaifin yaron Mista […]

Zimbabwe: Soja sun kori yaro daga makaranta kan alakar babansa da Jam’iyyar MDC-T
Zimbabwe: Soja sun kori yaro daga makaranta kan alakar babansa da Jam’iyyar MDC-T

Sojoji sun kori wani yaro dan shekara biyar daga makaranta a kasar Zimbabwe saboda mahaifinsa na goyon bayan jam’iyyar adawa ta MDC-T.
Yaron mai suna, Enos Choga, yana makarantar share fagen shiga firamare ce a barikin 1 Commando Barracks wadda doka ta ce wajibi ne ta dauki dukkan yara ciki har na fararen hula.
Mahaifin yaron Mista Kubboruno Choga – Enos ya shaida wa gidan rediyon SW Radio Africa cewa yaron nasa ya saki jiki tare da samun abokai a makarantar kafin wannan lamari ya auku a Larabar makon jiya.
Ya ce gane cewa shi mahaifin yaron dan Jam’iyyar MDC-T ne kuma shi ne sakatarenta na gundumar Chirumanzu-Zibagwe da ke yankin Midlands ne ya jawo aukuwar hakan. Ya ce, “Kwanaki na dauki Enos zuwa makarantar, sai na hadu da wani sojan kasar Zimbabwe. Na san shi ya fito ne daga garin Mudzi inda nake zaune, kuma na yi suna a harkokin Jam’iyyar MDC-T.
Choga ya ce yana zargin wannan soja ne ya kai rahotonsa ga na gaba da shi, lamarin da ya sa wani jami’in soja mai suna Murakasha ya kira shi don yi masa tambayoyi a makon jiya.  “Sama da awa daya aka dauka ana yi min tambayoyi kan inda aka haife ni da iyayena da abin da nake yi a rayuwa. Na yi tunanin wani abu na faruwa ba daidai ba, domin ba wadannan tambayoyi ne ya kamata dan kwamtin wata makaranta ya yi wa mahaifin dan makaranta ba. Na fada musu gaskiya. Amma jm kadan da barin makarantar sojan nan ya sake kirana cewa gobe in dawo tare da kananan hotunana,” inji Choga.
Ya ce da ya fahimci ana jan magana sai ya shaida musu cewa shi dan Jam’iyyar MDC-T ne, kuma bayan haka ne shugaban makarantar ta yi masa waya cewa an kori Enos daga makarantar kuma za a mayar masa da kudinsa.
Sai dai lokacin da jaridar NewsDay ta tuntubi jami’an sojan sun musanta korar Enos. Kuma Murakasha ya shaida wa jaridar cewa magana kawai ya yi da mahaifin Enos, yayin da kakakin soja Alphios Makotore ya ce batun korar Enos karya ce da makiya ke yadawa.