Zirin Gaza: Indiya ta ba wa Falasdinawa kayan jinkai

Indiya ta tura ton 38.5 na kayan jinkai ga al’ummar Falasdinawa da hare-haren Isra’ila suka daidaita a Zirin Gaza

Zirin Gaza: Indiya ta ba wa Falasdinawa kayan jinkai

Wasu kayan ajagji da aka kai wa mutanen da rikicin Hamas da Isra’ila ta shafa a kasar Lebanon. (Hoto: Mahmoud Zayyat/AFP)

Indiya ta tura ton 38.5 na kayan abinci da magunguna da sauran kayan jinkai ga al’ummar Falasdinawa da hare-haren Isra’ila suka daidaita a Zirin Gaza.

A safiyar Lahadi Iniya ta tura jirgin sojinta dauke da kayan zuwa yankin Sinai na kasar Masar, inda daga nan za a tsallaka da su zuwa Zirin Gaza.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Indiya, Arindam Bagchi, ya ce kayan sun hada da: “tantuna da shinfidu da mayafai, da sabulai na sinadaran tsaftace ruwa da tampol da dai sauransu”.

Ranar Asabar aka fara shigar da kayan jinkai ga Falasdinawa ta mashigar Rafah da ke karkashin kulawar kasar Masar, ta hannun kungiyar jinkai ta Red Crescent.

Kungiyar ta bayyana rukunin farko na motoci 20 da suka fara shiga yankin Zirin Gaza a matsayin abin da bai kai cikin cokali na kayan agaji da ake bukata a yankin ba.

Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 4,300 akasarinsu fararen hula, mata da kananan yara da tsofaffi a Zirin Gaza, inda ta jikkata wasu 13,000 a mako makonni biyu da ta kwashe tana wa yankin luguden wuta.

Sama da mako guda ke nan da Isra’ila ta yanke wa Zirin Gaza ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin sufuri tare da hana shiga da fita a yankin, da sunan samame don murkushe kungiyar Hamas.

A makon jiya ta kai hari da ya hallaka fararen hula kimanin 500 a wani asibiti da ke Kudancin Zirin Gaza, bayan da ta umarci Falasdinawa da su koma yankin da zama.

Sama da Falasdinawa miliyan daya ne jiragen Isra’ila suka yi lebur da gidajensu a Zirin Gaza, yankin da ke da mazauna kimanin miliyan 2.4.

Isra’ila wadda sojojinta ke shirin kutsawa cikin Zirin Gaza da kasa ta kaddamar da hare-haren jiragen ne bayan kazamin harin da kungiyar Falasdinawa ta ta Hamas ta kai mata, inda mayakan kungiyar suka kashe mutum 1,400 suka yi garkuwa da wasu kimanin 200.

Indiya ta yi tir da harin na Hamas, amma ta jaddada bukatar kafa kasar Falasdinawa mai cikakken ’yanci.