Ziyara

Wani Bafillatani ne za su je ziyara ganin gidan surukansa, shi da matarsa. Sun zo daf da kofar gidan surukan nasa sai tusa ta kwace masa ta yi kara sai ya ja yat saya. Ya ce wa matarsa: “Yau fa an yi abun kunya, ba zan shiga gidan nan ba sai kin je kin tambayo, […]

Ziyara
Ziyara

Wani Bafillatani ne za su je ziyara ganin gidan surukansa, shi da matarsa. Sun zo daf da kofar gidan surukan nasa sai tusa ta kwace masa ta yi kara sai ya ja yat saya. Ya ce wa matarsa: “Yau fa an yi abun kunya, ba zan shiga gidan nan ba sai kin je kin tambayo, ko sun ji karar tusar nan kuwa? Idan ba su ji ba, in shiga amma in sun ji to fa a waje zan tsaya, ba zan shiga ba. Sai matar ta shiga ta tambaya, ta ce: “Mun zo tare da mijina ne amma ya ce ba zai shigo ba sai na tambaye ku ko kun ji karar tusarsa ko ba ku ji ba?” Sai surukar ta ce: “Ba mu ji ba.” Da matar ta dawo ta gaya masa cewa ba su ji karar ba sai ya shiga.

Daga Mamunu Abubakar Kafin Madaki, 08033708347.

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 sun sace dabbobi a Bakori