Ziyarar Babban limamin Ingila alheri ne ga Najeriya – Limamin Sultan Bello
A kwanakin baya ne masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna, ya gayyato Limamin babban masallacin kasar Ingila da ke birnin Landan Sheikh Khalifa Izzat zuwa Najeriya. A wannan tattaunawa da wakilinmu ya yi da babban Limamin masallacin sultan Bello Sheikh Muhammad Sulaiman, ya bayyana abubuwan da suka sanya suka gayyaci wannan limami da abubuwan […]
A kwanakin baya ne masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna, ya gayyato Limamin babban masallacin kasar Ingila da ke birnin Landan Sheikh Khalifa Izzat zuwa Najeriya. A wannan tattaunawa da wakilinmu ya yi da babban Limamin masallacin sultan Bello Sheikh Muhammad Sulaiman, ya bayyana abubuwan da suka sanya suka gayyaci wannan limami da abubuwan da ya yi a ziyarar da kuma irin fa’idojin da aka samu a wannan ziyara. Ga yadda tattaunawar ta kasance
Aminiya; Meye ya karfafawa masallacin Sultan Bello gwiwa wajen gayyato Limamin babban masallacin kasar Ingila, da ke birnin Landan Sheikh Khalifah Izzat zuwa nan Najeriya?
Sheikh Sulaiman; Abin da ya karfafa mana gwiwar gayyato wannan babban limami na kasar Ingila zuwa nan Najeriya, abubuwa ne kamar guda uku. Na farko shi ne domin ganin masallacin Sultan Bello ya kasance yana da matsayi, kamar sauran manyan masallatan duniya. Na biyu kwarewar da kasashen turai suke da shi, a bangaren gudanarwa ya sha banban da irin namu, saboda suna da wayewa. Don haka zuwan wannan limami za mu tattauna abubuwa da za su kawo wa wannan masallaci cigaba. Abu na uku shi ne samar da hanyoyin bayar da guraben karatu tsakanin bangarorin guda biyu. Muna son masallacin Sultan Bello ya zama wata cibiya ta samar da guraben karatu ga yaran Najeriya, don su rika zuwa suna karo ilmi. Kuma muna son wannan masallaci ya zama wata cibiya da za ta rika gayyato malaman duniya don su rika zuwa suna ilmantar da mutanen Najeriya.
Aminiya; Kamar wadanne abubuwa ne wannan limami ya gabatar a wannan ziyara da ya kawo?
Sheikh Sulaiman; A Wannan ziyara ta kwanaki biyar da wannan babban limami na kasar Ingila Sheikh Khalifar Izzat ya kawo kasar nan, don hada dankon zumunci tsakanin babban masallacin kasar Ingila da masallacin Sultan Bello da kuma hada dankon zumunci tsakanin Najeriya da kasar Ingila. Tare da gabatar da jawabi kan addinin musulunci ga limamai da malamai da kungiyoyin addini ya gudanar da abubuwa masu tarin yawa.
Da farkon isowarsa Najeriya ya yi kwana daya a babban birnin tarayya Abuja. Inda ya ziyarci babban masallacin kasa, ya zagaya ya ga yadda tsarin masallacin yake. Kuma ya gabatar da lakcoci daban daban a masallacin ga kungiyoyin mata da sauran jama’a da ke sallah a masallacin.
Bayan haka ya yi taro da kungiyar limaman Abuja wadanda suka kai 350. Ya tattauna da su kan hanyoyin da’awa irin na zamani.
Daga nan ya taho garin Kaduna ya ziyarci masallacin tunawa da marigayi Sheikh Jafar Adam ya gabatar da lacca, kan yadda limamai da ladanai za su dogara da kansu, ta yadda ba sai sun dogara da wani ba.
Daga nan ya zo babban masallacin Sultan Bello ya gabatar da babbar laccar da ta kawo shi Najeriya, mai taken gudunmawar da limamai za su bayar wajen ci gaban tattalin arzikin kasa da kawo aminci da kwanciyar hankali da tsaro a cikin kasa.
Daga nan kuma ya je masallacin Almannar ya gabatar da wata lacca kan kyawawan dabi’u da ya kamata mai da’awa da limamai su kasance suna yi.
Bayan haka ya yi zama da dukan kungiyoyin mata musulmi na garin Kaduna ya tattauna da su, ya basu shawarwari kan yadda za su hada kansu su taimaki kansu wajen gudanar da ayyukansu.
Daga nan ya kai ziyara gidan Gwamnatin Jihar Kaduna inda sakataren gwamnatin jihar ya karbe shi, suka tattauna kan yadda za a rika samun musayar tallafin guraben karatu ga daliban Najeriya da kasar Ingila da sauran hanyoyin bunkasa wadannan kasashe.
Daga nan ya wuce fadar Mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya kai masa ziyara, inda Mai martaba ya karramashi aka yi masa nadi aka sanya masa babbar riga. Shi kuma ya bai wa Mai martaba kyautar wasu littafai da ya rubuta.
Daga nan muka wuce Kano, ya ziyarci masallacin Alfurkan ya gabatar da lacca kan muhimmancin kafofin yada labarai da suka hada da jaridu da gidajen rediyo da talbijin da sauran kafofin sadarwa na yanar gizo. Ya yi bayanin yadda malamai za su bada muhimmanci kan wannan bangare don ilmantar da jama’a.
Daga nan ya ziyarci wasu manya malamai a garin na Kano, daga nan ya kammala wannan ziyara, aka yi sallama ya koma gida.
Aminiya; Kamar wadanne irin fa’idoji ne kake ganin an samu kan wannan ziyara?
Sheikh Sulaiman; A gaskiya fa’idojin da aka samu suna da yawa, fa’ida ta farko shi ne wayar da kan al’ummarmu. Fa’ida ta biyu dukan laccacin da wannan limami ya gabatar laccoci ne da za su amfani dukkan al’ummar musulmi da wadanda ma ba musulmi ba. Domin ya gabatar da lacca kan miyagun maganganu, idan ka lura abokanan zamanmu suna kyamar miyagun maganganun da ake jifarsu da su.
Fa’ida ta gaba ita ce wata kila suma su gayyaci wasu malamai sakamakon wannan gayyata da aka yi wa wannan limami. Musamman limamin wannan masallaci na Sultan Bello, don shi ma ya je ya gaya yadda suke gudanar da ayyukansu da tsare-tsarensu. Fa’ida ta gaba kuma ita ce za a sami taimakekeniya a tsakaninmu. Kamar tallafin guraben karatu da ake bayarwa.
Aminiya; Ya zuwa wadanne irin ayyuka ne wannan masallaci ya sanya a gaba?
Sheikh Sulaiman; To a ‘yan kwanakin nan akwai wani taron kara wa juna sani, na kasa da kasa da wannan masallaci ya shirya na kwanaki uku. Wannan taron kara wa juna sani an shiryawa makarantun da suke koyar da addinin musulunci ne.
An sami kwararrun malamai wajen karatarwa da tarbiyatarwa kan irin wadannan fannoni guda 3. daya daga kasar Saudi Arabiya daya daga kasar Masar dayan kuma daga nan Najeriya. Wadannan malamai ne suka karantar da mahalarta wannan taro. Kuma mutum 80 ne da suka fito daga Jihohin Gombe, Taraba, Bauchi, Filato, Adamawa, Kano, Zamfara, Kebbi, Sakkwato, Kaduna, babban birnin tarayya Abuja suka halarci wajen wannan taro.
Abin da ya karfafawa wannan masallaci gwiwar shirya irin wadannan tarurruka shi ne saboda matsayin wannan masallaci na Arewa gabaki daya, idan ba a kira shi na Najeriya gabaki daya ba. Saboda a lokacin da aka gina wannan masallaci Kaduna ita ce hedkwatar Jihar Arewa gabaki daya.
Kuma masallaci ba aikin shi ne kadai ayi sallah a rufe shi ba. Yana daga cikin manufar wannan masallaci ya taimakawa al’umma ta kowane bangaren rayuwa. Kaga ana karatuttuka na wa’azi, amma bangaren makarantu gudunmawar da masallaci zai bayar shi ne musamman a wannan lokaci da gwamnatin Jihar Kaduna ta fito da tsarin cewa tana son ta sami kwararrun malaman makarantu a makarantun gwamnati da sauran makarantu gabaki daya. Wannan ne ya karfafawa wannan masallaci gwiwa a inda hukumar gudanarwar masallacin tare da ofishin limamin masallacin suka shirya wannan taron bita, don bada gudunmawa ga al’umma.
Bayan haka wannan masallaci ya sanya tsarin tsaftace shi da canza masa shinfudu da fenti.
Kuma wannan masallaci ya dauki nauyin karatun wasu marayu ya tura su je su koyo jinyar hakora da tsaftar gari.
Haka kuma wannan masallaci ya sanya aikin koyar da karatun Alku’ani mai girma a gaba, don haka ya bude makarantun koyar da Alkura’ani na yara da mata da wadanda suka kware da kuma wadanda suke koyo, daban daban har guda 19 a wannan masallaci. Nan gaba kuma za mu bude sashin koyon larabci daban daban.
Haka kuma a wannan masallaci a kullum ana karantarwa. Akwai koyarwa da ake yi bayan sallar la’asar a kullum, kuma a duk ranar lahadi Dokta Ahmed Abubakar Muhmud Gumi yana karantar da Muwadda haka kuma Sheikh Abubakar Usman Babantine yana karantar da fikihu a duk ranar juma’a kuma akwai katatuttuka da ake yi a kullum na littafai daban daban a tsakanin Sallar mariba da isha. Don haka muna kira ga jama’a su rika zuwa suna saurara don su rika amfana.