Ziyarar birkitaccen gidan kasar Austiriya
Ba da dadewa ba na samu labarin birkitaccen gida a garin Terfen da ke kasar Austiriya Wannan labara ne mai matukar ban mamaki ga duk wanda ya ji shi, domin a lokacin da ake bayar da bayanai a kan gidan da wuya mutum ya iya boye mamakin da yake cike da shi. Nan take sai […]
Ba da dadewa ba na samu labarin birkitaccen gida a garin Terfen da ke kasar Austiriya Wannan labara ne mai matukar ban mamaki ga duk wanda ya ji shi, domin a lokacin da ake bayar da bayanai a kan gidan da wuya mutum ya iya boye mamakin da yake cike da shi. Nan take sai aka dauke ni da yamma zuwa wannan gida, don in gane wa idona Tafiyar dai ta kimanin minti 15 ce daga matsugunnin Grail da ke garin bomperberg, a garin da na sauka cikin makon karshe a watan Mayu. Akwai tituna masu kyau a daukacin fadin Austiriya, sannan akwai titin jirgin kasa mai inganci. Ga kuma yanayi mai kyau da furanni da nau’ukan tasirrai masu ban sha’awa da kuma duwatsu kewaye da ko’ina. Cikin kankanen lokaci sai muka sauka a gaban birkitaccen gida, wanda muka tabbatar a jirkice yake, kuma an gina shi ne a irin wannan tsarin don haka ake son ganinsa.
Duk wanda zai shiga gidan sai ya biya kudi Yuro shida, wannan kuwa ba wani abin damuwa ba ne. saboda irin kayatarwar da gidan ke da shi ga duk wanda ya kewaya cikinsa. Wannan gini ya birkita tsarin yadda ya kamata a tsara gida. An kawata cikin gidan da kayan alatu, wadanda aka birkita a like jikin rufin gidan. Mai karatu zai iya fahimtar cewa tushen ginin gidan yana kallon sama. Sabanin yadda ake tsammanin tebur zai kasance a kasan daki, amma sai ga shi a wata birkitattar duniya, tka yadda tebura ke like a jikin silin din daki.
Matsugunnin kashi a bayi ba a kasa yake ba, don tana like ne a jikin silin.
Murhun girki da gadon yara duk a like suke a saman silin, maimakon a kasan daben daki, ta yadda daukacinw adannan al’amura za su jefa iyaye cikin tashin hankali, matukkar akwai mazaunan da ke cikin gidan. Motar da ke ajiye a gareji, ita ma a like take a saman silin, al’amarin da zai rikita tunanin direba. daukacin kayan alatun gidan an girke su a wurin da bai kamata a ce an same su ba, duk da cewa suna kayatar da mai ziyara, tsoho ne ko matashi.
Akwai abubuwan ban dariya game da tsarin kayan alatun gidan. Alal misali bandakin gidan a birkice yake. Wannan dai na nuni da wani tsari na duniya da komai a birkice yake, al’amarin da ke nuni da karin cukurkudewar al’amuran da ke cike da ban mamaki da mutum kan smau kansa a cikinsu.
Tabbas fasalin wannan gida ya yi tasiri wajen sanya masu ziyara ya shiga tunanin kan rayuwar zamani.
Birkitaccen gida Terfen, wadanda suka gina shi , shi ne Irek Glowacki da Marek Rozhanski, wasu kwararrun masu zayyana ’yan asalin Poland, wadanda suka shafe watanni takwas suna tsara fasalin gini, al’amarin da suka aiwatar da manufar jawo hankali masu yawon bude ido zuwa wannan wuri.
Daga bisani na hadu da wani dan uwana dan Najeriya, wand ake cike da farin ciki a lokacin da ya ba ni labarin wannan gida. Ya fake da cewa aikin wannan gida na nuni da cewa maginan na da dimbin kudin da suke bukatar salwantarwa. Ni dai ban yarda da ra’ayinsa ba, domin a ganina, wannan aiki ne na ’yan baiwa masu dimbin basira, da tsarin shirya biki a fagen zayyana, da ke nuni da hargitsattsen tsari da al’amuran da ke da wuyar tabbata a rayuwar mutumin zamani.
Lallai mai karatu ya fhaimci cewa, wannan gida na alfarma na nuni da kawace-kawacen zamani, ko wani shirmen zahiri, amma duk da haka wannan aiki ya cancanci yabo, ko da a ce an yi nufin salwantar da kudi ne. Idan har ka ziyarci birkitaccen gida, to ka shirya jin juwa-juwa, al’amarin da kan far wa masu ziyara a lokacin da suke kewaya wannan gida mai rikitar da tunani da juyin duniya, ta yadda (ni ke ganin) jemage ba zai samu matsala da shi ba.
karkarewar bayanai: Lokacin da na kammala ziyarar wannan gida mai ban mamaki, sai dubniyar da nike ciki ta juye mini kasa da sama. Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyyar rasa tasi da za ta dawo da ni masaukina ake Matsugunnin Grail. Na tsaya a kan titi, inda na yi ta kai kawo a tunanina kan dalilin da ya sanya tun farko ma na yanke shawarar kai ziyara wnanan gida. Na dan shiga rudu, saboda ban iya Magana da Jamusanci sosai ba. Ina ta tunanin ko zan samu wanda ya yi magana da Turancin Ingilishi? Daga bisani na hadu da Mista Hannes Niederlecher, wanda na yi sa’ar jin cewa ya iya magana da Ingilishi. Bayan da ya saurare ni, sai ya dauki nauyin daukata a motarsa zuwa masaukina ba tare da na biya komai ba, tunda ya fahimci akwai wahalar samun tasi a daidai inda muke. Sai ya sanar da matarsa, wadda ta daga mini hannu tana gaishe ni.
Sai muka tafi cikin farin ciki, ina zaune a bayan motar. Ina cike da farin ciki samun mai kirki a wannan kasa da na kai ziyara a karo na farko. Irin wannan kyakkyawan hali da kirkin da aka yi mini, shin mai zai hana in ce Austiriya kasar mutanen kirki ce? Ina fatan sake kai ziyara kasar Austiriya, inda zan sake zuwa in gaishe da abokina Niederlecher.