Ziyarar Buhari Borno: An tsaurara tsaro a Maiduguri

An tsananta tsaro a birnin Maiduguri da kewayen ta a jihar Borno don ziyarar da Shugaban Najeriya ke yi a jihar. Da kuma halartar taron sojojin Najeriya na rubu’in shekara da ake yi yau a jihar. Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ce, wannan ne karon farko da shugaban kasar ya halarci taron tun lokacin […]

Ziyarar Buhari Borno: An tsaurara tsaro a Maiduguri

An tsananta tsaro a birnin Maiduguri da kewayen ta a jihar Borno don ziyarar da Shugaban Najeriya ke yi a jihar. Da kuma halartar taron sojojin Najeriya na rubu’in shekara da ake yi yau a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ce, wannan ne karon farko da shugaban kasar ya halarci taron tun lokacin da ya fara mulkin a shekarar 2015.

An shirya taron sojojin Najeriya da nufin bitan ayyukan rundunar sojojin Najeriya wadanda suka hada da: yadda ake gudanar da harkokin jami’an tsaron da bullo da hanyar inganta ayyukansu wajen tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya.