Ziyarar Jami’ar Wukari ga NCC zai haifar da da mai ido
A kwanan nan ne Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta karbi bakuncin manyan jami’an gudanarwar Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Wukari dake Jihar Taraba. Shugaban Jami’ar, Alhaji Ahmed Uba Nana (Garkunwan Ningi) ya ambaci daruruwan gudunmawar da hukumar NCC ta bayar wajen sake fasalin harkokin sadarwa zuwa na zamani, inda ya kara da cewa, nadin Farfesa […]
A kwanan nan ne Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta karbi bakuncin manyan jami’an gudanarwar Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Wukari dake Jihar Taraba.
Shugaban Jami’ar, Alhaji Ahmed Uba Nana (Garkunwan Ningi) ya ambaci daruruwan gudunmawar da hukumar NCC ta bayar wajen sake fasalin harkokin sadarwa zuwa na zamani, inda ya kara da cewa, nadin Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin shugaban hukumar abin jinjinawa ne wanda kuma ya dace.
Sannan ya ce Jami’ar Wukari ta na daga cikin jami’o’in da Gwamnatin Tarayya ta kirkira a shekarar 2011 a bisa kokarinta na daga darajar ilimi a Najeriya. A yunkurinta na cimma nasarar manufofinta, jami’ar ta samar da wasu shirye-shirye da za su taimaka wajen gina daidaiku a fannonin kimiyyar labarai da sadarwa.
Don haka amfanun wadannan abubuwa biyu, ba abinda za kawar da kai kansu ba ne. Sannan sai ya bayyana cewa ziyarar tasu ga hukumar don karfafa gwiwa ce bisa yadda jami’ar ta dukufa wajen sake fasalin kimiyyar sadarwa don cimma ingantaccen tsari don ida cika muradunta, tare da samar da kayakin aikin da suka hada kwamfutocin hannu da na tebur a dukkan dakunan kimiyyar jami’ar.
Ya kuma kara da cewa “Gudunmawarka ga manufofin jami’armu ta fuskar fasaha da kuma inganta ilmi a Najeriya ya kai ga tasirin da yake amfanar al’ummarmu baki daya musamman a jami’o’i.”
A yayin da yake maida jawabi, Shugaban Hukumar Sadarwa na Najeriya, Farfesa Umar Garba Danbatta, yay i nuni da wasu daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta samar don kafafa harkokin labarai da sadarwa a makarantu wadanda kudurorinsa guda 8 suka kunsa.
Tun da farko a jawabinsa, Sakataren USPF, Mista Ayuba Shuaibu ya bayyana cewa tuni wannan hukuma ta aike da tawagar mutane biyu zuwa jami’ar don jin bukatunsu da kuma yadda hukumar za ta taimaka masu. Ya kuma kara da cewa shirye-shirye irinsu (TIKC), da (ADAPTI) suna daga cikin daukin da wannan hukuma ta ke kaiwa don taimakawa jami’o’i ta fuskar cimma yada labarai da sadarwa.
Mataimakin Daraktan Sababbin kafofi da labaran sha’anin tsaro na NCC, Dakta Henry Nkemadu, ya bayyana cewa hukumar tana tallafa wa jami’o’i da kayayyakin ICT a duk shekara, sai y ace amma an riga an sanya shekarar 2018 cikin kasafi, amma duk da haka akwai wasu damarmki da a iya riska a shekara mai zuwa.