Ziyarar Jonathan da Sheriff zuwa Chadi ta tada kura

Ziyarar da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kai tare da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff zuwa kasar Chadi ta tayar da kura, sakamakon fusatar da wasu ’yan Najeriya suka yi kan yadda Shugaban kasar ya tafi da Sheriff din a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen a bincike shi kan zargin hannunsa […]

Ziyarar Jonathan da Sheriff zuwa Chadi ta tada kura

Ziyarar da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kai tare da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff zuwa kasar Chadi ta tayar da kura, sakamakon fusatar da wasu ’yan Najeriya suka yi kan yadda Shugaban kasar ya tafi da Sheriff din a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen a bincike shi kan zargin hannunsa a tallafa wa Boko Haram.
 A wata sanarwa da babbar jam’iyyar adawa ta APC ta fitar ta soki Shugaba Jonathan da aikata “Abu mai tayar da hankali na rungumar wanda ake zargi da tallafa wa Boko Haram. Wannan aiki na Shugaban kasa ya tabbatar da abin da APC ta yi yakini cewa, Shugaban kasar ko dai ya san wadanda suke da hannu a hare-haren Boko Haram amma ya gaza fallasa su, ko kuma ya gwammace ya sarayar da yaki da ’yan ta’adda domin cimma wata manufa ta siyasa,” inji APC.
Jam’iyyar APC ta ce: “Koma mene ne, abin da Shugaban kasar ya yi, babban tabargaza ce da nuna rashin ya kamata. Idan ma wannan wasa ne, to an wuce iyaka, musamman a wannan lokaci da Najeriya ke rasa yankunanta ga Boko Haram; kuma a lokacin da wata majiya ta mashawarcin Najeriya kan harkar tsaro a Chadi ke zargin Modu Sheriff da hannu a harkar Boko Haram, kuma a lokacin da ake kiraye-kirayen a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan zargin da ake yi wa Modu Sheriff da tsoho Hafsan Hafsoshin Najeriya Azubuike Ihejirika na tallafa wa Boko Haram.
Sheriff dai ya musanta zargin alaka da kungiyar Boko Haram.
Wata jaridar Kamaru mai suna L’Oriel du Sahel, ta buga a ranar 2 ga Afrilu, 2012 cewa an kama tsohon Gwamnan wanda yanzu dan Jam’iyyar PDP ne, lokacin da ya shiga Kamaru daga Chadi, a kan hanyarsa ta zuwa don ganawa da Gwamnan Arewacin kasar ta Kamaru.
Rahoton ya ce, mahukuntan ’yan sandan Kamaru sun tuhumi Sheriff na tsawo awoyi, kuma an sake shi ne bayan matsi daga manyan jami’an gwamnatin kasar.
A ranar Litinin ne Shugaba Jonathan ya gana da takwaransa na Chadi a birnin Ndjamena, tare da tsohon Gwamna Modu Sheriff.
 Wani hoto da FaDA Shugaban kasa ta fitar a ranar Talata ya nuna Sheriff a zaune a wurin wani muhimmin taro kan tsaro tare da Shugaba Idris Derby na kasar Chadi.
Bayan farko na fadar Shugaban kasa, sun ce, an tattauna ne kan yadda za a karfafa yarjejeniyoyin da ake cimma a baya a tsakanin Najeriya da makwabtanta dangane da sintiri a kan iyakokin kasashen da musayar bayanan sirri da dakile kai-kawon ’yan ta’adda da makamai a kan iyakokin.
Ganawar kuma ta tabo tattaunawar da aka yi a Nairobin kasar Kenya na makon jiya wajen taron Kwamitin Tsaro na Tarayyar Afirka da Shugaba Derby wanda shi ne shugaban majalisar ya halarta.
Ganawar ta zo ne a lokacin da ’yan Najeriya ke kiran a binciki Sheriff da Ihejirika sakamakon zarginsu da wani dan Autireliya mai shiga tsakani ya yi da tallafa wa Boko Haram, wadda ta jawo hallaka mutum dubu 13.
Kakakin Hukumar Tsaro ta kasa (SSS), Marilyn Ogar, ta yi fatali da zargin da ake yi wa Ihejirika amma ta ce an taba tuhumar Sheriff a baya kan alaka da ’yan ta’adda, kuma za a sake tuhumarsa kan zargin na bayan nan.
Daga farko fadar Shugaban kasa ta ce cikin ’yan rakiyarsa akwai Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro, Sambo Dasuki da Ministan Sadarwa, Omobola Johnson da Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Nurudeen Mohammed da Darkta Janar na Hukumar Binciken Sararin Samaniya, Sa’idu Mohammed.
Sai dai hotunnan da aka sanya a shafin Twitter na Kakakin Shugaban kasa, Abati sun nuna Jonathan ya samu gagarumar tarba daga ’yan Najeriya a Ndjamena, kuma daga baya ya shiga ganawa da Shugaba Derby da Modu Sheriff.
‘Yan Najeriya da dama sun soki ziyarar Shugaban tare da Sheriff a shafukansu na Facebook da Tweeter.