Ziyarar Shugaba Jonathan Maiduguri ta jaje ce ko ta kamfen?

Tun da dadewa ake ta korafin cewa ya kamata Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai ziyara Jihar Borno domin jajanta wa wadanda masifar Boko Haram ta addaba, amma bai je ba sai a makon jiya, inda ya rage kasa da wata guda a gudanar da zabe. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan ziyara […]

Ziyarar Shugaba Jonathan Maiduguri ta jaje ce ko ta kamfen?
Ziyarar Shugaba Jonathan Maiduguri ta jaje ce ko ta kamfen?

Tun da dadewa ake ta korafin cewa ya kamata Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai ziyara Jihar Borno domin jajanta wa wadanda masifar Boko Haram ta addaba, amma bai je ba sai a makon jiya, inda ya rage kasa da wata guda a gudanar da zabe. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan ziyara da ya kai Maiduguri, shin ta jajantawa ce ko kuwa ta yawon yakin neman zabe? Ga abin da mabambantan mutane ke cewa:

Kamfen ya je ba jaje ba – Aminu Abdullahi

Musa Kutama, a Kalaba

Aminu Abdullahi Bakori: “Eh! Ziyarar da Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kai Jihar Borno, kusan shekara biyar ana ta kashe bayin Allah, an sace ’yan matan Chibok bai je ba, ana ta daukar rayuwar bayin Allah ba dare ba rana; duk bai je ba sai yanzu lokacin kamfe sannan ya je. Kuma ma da ya tashi zuwa, ai barikin soja ya je, aka tattaro masa ’yan gudun hijira. Wannan kamfe ya je ba ziyarar jajanta wa mutanen Jihar Borno ya je ba.”

Yakin neman zabe je – Aminu Auwal

Musa Kutama, a Kalaba

Aminu Auwal Shehu: “Ba wani abu, ziyara ce ta dubara ya kai domin ya yi kamfen. Ai da can ya taba cewa zai kai ziyarar domin jajanta wa al’ummar Jihar Borno amma sai ya karkata ta zuwa kasar waje, bai je can ba. Don haka kamfe ya je yi ba ziyarar jajantawa ba.”

Ba ziyarar jaje ba ce – Alhaji Gambo

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Alhaji Gambo Chiral-Waral: “A ganina, batun nan na kai ziyara da Shugaban kasa Jonathan ya yi a garin Maiduguri, ba ziyarar jaje ya kai ba, ya je ne don yin yakin neman sake zabensa a fakaice. Dalilin fadar haka kuwa shi ne, ai in da da gaske yake yi, na ya damu da rayuwar al’ummar Borno da ma na yankunan Arewa; ai da tun tuni ya kai wannan ziyara ta jaje amma da yake da wata manufa, ai ka ga ya fake ne da ziyara don yakin neman zabe.
“Don haka mu kan ba mu yarda da cewar Shugaban kasar ya je Maiduguri ba ne don ziyarar jaje, ya je ne kawai don bukatar kansa ta yakin neman zabe. Fakat!”

Ya fake da ziyarar jaje amma… – Shugaba Maccido

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Shugaba Maccido Apollo: “A ganina, wannan ziyara da Shugaban kasa ya kai a garin Maiduguri, ba komai ba ne illa fakewa da ziyarar don yin abin da ya fi damunsa, wato kamfen. Domin in har da shi Shugaban kasar ya damu da al’ummomin Jihar Borno da ma na sauran wuraren suke fama da wannan rikita-rikita, ai da ya dade da kai musu wannan irin ziyara ta jaje ba wai sai yanzu ba da lokacin zabe ya karato ba. Don haka a fada masa cewa kifi na ganinka mai jar koma.

Kamfen ne ba jaje ba – Saifullahi Abdullahi

Lubabtu I. Garba a Kano

Saifullahi Abdullahi: “Kowa ya san abin da ya kai Shugaban kasa Goodluck Jonathan garin Maiduguri, wato neman kuri’a. Idan aka yi la’akari da abubuwa na rashin dadi da suka yi ta faruwa a lokutan baya, wadanda ma suka fi na yanzu muni amma bai je ya yi wa al’ummar jihar jaje ba, wai sai a wanann lokaci da ya ga zabe ya kusanto. Sanann abin bakin cikin ma, bai karasa wurin al’ummar garin, wadanda abin ya shafa kai tsaye ya yi musus jajen ba; sai ya tsaya a wani wuri. Lokacin da ya gama abin da zai yi, ya yi tafiyarsa abinsa ba tare da ya je ya gan su ba.”

Yakin neman zabe ya je yi – Adda’u Ibrahim

Lubabatu I. Garba a Kano

Adda’u Ibrahim: “Babu abin da ya kai Shugaban kasa Jonathan Jihar Borno illa yakin neman zabe, kasancewar kakar zabe ta zo, yana neman kuri’ar mutanen garin; shi ne ya fake da batun yi musu jaje. Idan jaje zai yi musu, me ya sa bai je ba alokacin da aka yi ta kai musu munanan hare-hare, musamamn lokacin da aka sace ’yan matan Chibok? A matsayinsa na shugaba wanda shi ne jagora, ya kamata a ce tuni ya jajanta wa wadannan al’umma da musibar rashin kwanciyar hankali ta addabe su. Ina ganin ai Jonathan ba shi da kuri’a ko guda daya a Maiduguri, idan aka yi la’akari da yadda ya yi watsi da lamurran al’umara jihar a lokacin da suke da bukatar taimakonsa.”