Ziyarar ‘yar Buhari Bauchi ya bar baya da kura
Tun bayan ziyarar ‘yar Shugaba Buhari, Hanan Buhari, zuwa jihar Bauchi ranar Juma’a a jirgin shugaban kasar Najeriya, da nufin halartar wasannin gargajiya da al’adu da aka saba gudanarwa duk shekara a fadar gwamnatin jihar Bauchi. Wannan ziyarar ta Hanan Buhari, ta bar baya da kura bayan wasu masu sharhi a shafukan sadarwa na zamani […]
Hanan Buhari a filin jirgin saman Bauchi
Tun bayan ziyarar ‘yar Shugaba Buhari, Hanan Buhari, zuwa jihar Bauchi ranar Juma’a a jirgin shugaban kasar Najeriya, da nufin halartar wasannin gargajiya da al’adu da aka saba gudanarwa duk shekara a fadar gwamnatin jihar Bauchi.
Wannan ziyarar ta Hanan Buhari, ta bar baya da kura bayan wasu masu sharhi a shafukan sadarwa na zamani keta tafka muhawara, saboda amfani da jirgin saman da ‘yar Shugaban tayi.
Wasu na ganin amfani da jirgin bai dace ba, yayin da a wani bangaren fadar shugaban kasar suka bayar da martanin cewa, Hanan nada ‘yancin amfani da jirgin saman. Wani kuwa cewa ya yi Hanan, na cikin iyalan Shugaban kasar ba wani abu bane.
Hanan Buhari, ta samu kyakkyawar tarba cikin girmamawa daga uwar gidan Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Aishatu Bala Muhammad a fadar gwamnatin jihar Bauchi.
Hanan Buhari tare da sauran ‘yan tawagarta sun kai ziyarar ban girma da girmamawa ga Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu.
Ga yadda muhawarar ta kasance
“SAMAN a shafinsa na tiwita cewa ya yi a kasa ta Najeriya karamar ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Hanan Buhari, ta ziyarci Bauchi a jirgin shugaban kasa saboda amsa gayyatar Sarkin Bauchi GASKIA AN RAINA MU !!”
I pledge to Nigeria 🇳🇬 my country to be faithful loyal and Honest 🤗👇🏼 the youngest Daughter of Muhammadu Buhari in person of Hanan Buhari visited Bauchi on a Presidential Jet to attend Durban organized in her honor by the Emir himself 😃😃 GASKIA AN RAINA MU !! pic.twitter.com/OVhbFqCERl
— Mal. Salman I (@Salmanlaure) January 11, 2020
“Hanan Buhari, a yanzu tana amfani da jirgin shugaban kasa. Duk da yake an fada mana cewa a shekarar 2016 ana shirin sayar da jirgin saman don rage kashe kudade. Amma yanzu ‘yar shugaban kasa na amfani da shi.”
So Hanan Buhari is now cruising with our Presidential flight. Though we were told in 2016 that there was a plan to sell them inorder to reduce cost, but now his daughter, despite the fact that he's regarded as the "Man of Integrity" is using one of them. pic.twitter.com/lHAIqrMOAy
— #FreeDadiyata🔴 (@Kabir_Kb1) January 10, 2020
“Jameel kuwa cewa, ya yi amfani da jirgin saman da Hanan tayi ba wani abu bane saboda tana cikin iyalan shugaban kasa, kuma jirgin saman ba a mallaka shi cewa shugaban kasa ne kadai zai iya amfani da shi ba. Hanan, tana daya daga cikin iyalan shugaban kasar. Banga dalilin da zaisa ‘yan Najeriya zasu yi ta muhawara akan wannan ba.”
https://twitter.com/Jameel31497573/status/1215978303141576704

Hanan Buhari, lokacin da take daukar hoto.